1
Menu
News

Kadarorin Diezani da na wasu ƴan siyasa da gwamnatin Najeriya za ta yi gwanjonsu

Wed, 27 Oct 2021 Source: www.bbc.com

Gwamnatin Najeriya ta fara shirin tantance darajar ƙadarorin da ta ƙwace ciki har da na wasu 'yan siyasa da suka hada da tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke.

Kadarorin Diezani da ke Banana Island, daya daga cikin unguwanni masu tsada a Legas sun hada da gidaje 24.

Gwamnatin Najeriyar ta dauki matakin ne bayan da kotuna suka kammala tabbatar mata da ƙwace kadarorin.

A watan Mayu shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya gaya wa majalisar wakilai cewa darajar sarkoki da awarwaro da sauran kayan ƙawa da aka ƙwace daga wurin Diezani ta kai naira biliyan 14.

Wasu daga cikin fitattun kadarorin da kotu ta kwace kuma sun hada da na marigayi tsohon hafsan hafsoshin tsaro na Najeriyar, Air Chief Marshal Alex Badeh, da ke unguwannin masu hali na Wuse 2 da Maitama.

Gidajen sun hada da mai lamba 14 Adzope Crescent, daura da Kumasi Crescent, da mai lamba 19 Kumasi Crescent, Wuse 2, da kuma gida mai lamba 6 Umme Street, Wuse 2.

Karin wasu daga cikin kadarorin da aka ƙwace wadanda ake tantance darajar tasu akwai rigunan bikin aure na musamman 125 da wasu kanana rugunan suma na musamman 13.

Akwai belet na boye tumbi 41 (domin fitar da surar mace) da furanni 73 na roba na musamman da kwat-kwat na mata 11 da rigar nono maras hannu guda 11 da gyale 73.

Sai kuma tarin rigar nono ta musamman guda 30 da fankar tsaye biyu da kayan masu sihiri 17 da fakiti shida na bargo da bargo na tebur daya da kuma takalma 64.

Daman tun a makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta fara tantance kamfanoni masu zaman kansu 613 masu neman a ba su kwangilar tantance kima ko kudin kayayyaki da kadarorin da kotuna suka mallaka mata bayan kwacewa, wadanda suke a wurare 25 a fadin kasar

Jumullar kadarorin da aka ware domin a yi gwanjonsu a fadin kasar sun kai 1,620, wadanda suka hada da motoci da gidaje da wayoyin salula da kwamfutoci na hannu da jiragen ruwa da sauran kayayyaki.

Mafi yawan kayayyakin da za a yi gwanjon suna Lagos, inda suka hada da gidaje 31 da motoci 589.

A makon da ya gabata ne shugaban kwamitin musamman na gwanjon kadarorin, Mohammed Etsu, ya fada wa 'yan jarida cewa an karbi takardun kamfanoni 229 da suka nemi kwangilar tantantace darajar kadarorin da suka kunshi injinan bayar da lantarki (jannareto) da na'urori da motoci da kujeru da tebura da makamantansu.

Kamfanoni 75 kuma ya ce sun gabatar da takardunsu na neman kwangilar tantance darajar jiragen ruwa, yayin da kamfanoni 25 suka gabatar da tasu bukatar kan tantance sarkoki da duwatsu na ado na mata da sauran kayan kawa da kuma tufafi.

Mohammed Etsu, wanda kuma shi ne babban mai kula da kararraki na Najeriya ya ce kwamitin zai yi aiki a bayyane a bisa gaskiya da amana wajen aikin.

Source: www.bbc.com
Related Articles: