News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ko rage man fetur da ƙasashen OPEC ke haƙowa zai shafi farashinsa a Najeriya?

Hoton alama

Tue, 6 Jun 2023 Source: BBC

Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin man Fetur ta OPEC tare da ƙawayenta sun amince da rage ganga miliyan 1.393 na man da suke fitarwa zuwa kasuwannin duniya a kowacce rana.

Duk da cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata Najeriya ba ta iya cika kasonta da ƙungiyar ta OPEC ta ware mata ba, sabon tsarin zai sake rage yawan fetur ɗin da Najeriyar ke fitarwa da kashi 20 cikin ɗari.

Hakan na nufin ƙasar za ta samu raguwa a yawan kuɗin shigarta.

Dama dai ƙasar na cikin ruɗani a ɓangaren na mai tun bayan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ‘tallafin man fetur ya kau.’

Haka nan kuma Najeriya, wadda ke shigo da tataccen man da take amfani da shi, da yiwuwar za ta yi fama da ƙarin farashin litar mai a ƙasar, kasancewar za a iya samun ƙarin yawan kuɗin da ake kashewa wajen shigo da tataccen man.

Wani masani kan man fetur, Kunle Adigun ya ce “Za a samu tashin farashin kaya a Najeriyar saboda farashin shigo da tataccen mai zai ƙaru, kuma hakan zai ƙare ne a kan al’umma kasancewar an cire tallafin man fetur.”

Matakin zai tilasta rage adadin man da Najeriya ke fitarwa da kashi 20.7 cikin 100.

Yarjejeniyar da ƙungiyar ta cimma bayan wani taro da ta gudanar a ƙarshen mako, ta tanadi cewa Najeriya wadda ke cikin mafiya arzikin man fetur a Afirka za ta rika fitar da ganga miliyan 1.380 a kowacce rana daga watan Janairu zuwa Disambar 2024.

Injiniya Yabagi Sani, wani masani a ɓangaren man fetur ya shaida wa BBC cewa wannan mataki babban koma-baya ne ga tattalin arziƙin Najeriya.

Ya ce "Wannan ba karamin koma-baya zai yi ma arziƙin Najeriya ba, saboda idan aka lura, ya zo ne a daidai lokacin da shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya janye tallafin mai, inda ko wane ɗan kasuwa zai iya sayo mai daga ƙasashen ƙetare ya kuma sayar ta yadda zai ci riba."

"Wato ke nan, ba NNPC kadai zai iya shigowa da mai ba, kowa yana iya yin hakan."

"To ke nan, za a buƙaci dalar Amurka fiye da yanda yake a da, shi ya sa muke cewa zai kawo matsala ga arziƙin Najeriya."

Yabagi ya kuma kara da cewa hukuncin zai sauko da karfin naira kuma hakan zai kawo karuwar farashin mai.

"Idan ba a sami dalar ba, zai shafi canji da ake yi, zai saka karfin naira ya je kasa, kuma hakan zai kawo karuwar na farashin mai da abubuwa da ake amfani da su a kasar saboda yawanci abubuwa da muke amfani da su, muna shigowa da su ne."

Ya kuma shawarci gwamnati da ta dauki mataki a kan masu satar mai.

"Shi ne ya sa muke cewa gwamnati ta tashi tsaye, ta duba, ta yi maganin sace-sacen mai da ake yi domin shi ne ya kawo Najeriya ta gaza fitar da ganga miliyan 1.826 da aka kebe mata."

"A takaice dai, wannan ragin da aka yi ya zo a lokacin da Najeriya ke buƙatar yadda za ta samu ƙarin shigowar kuɗin Amurka saboda irin abubuwan da sabuwar gwamnatin ta sanya a gaba, musamman kamar cire tallafin mai da kuma irin halin da arzikin kasar ya shiga."

Dama dai rahotonni na cewa ƙasar ba ta fitar da adadin man da OPEC ta keɓe mata, lamarin da masana ke ganin ya taimaka wajen rage kudin shigar da take samu daga sayar da man.

Source: BBC
Related Articles: