0
Menu
News

Matsalar rashin ilimi ce ke janyo koma-baya a Zangwannin Ghana - Ben Banda

Ministan Ma'aikatar Cigaban Zagwanni A Ghana, Muhammad Ben Banda.png Ministan Ma'aikatar Cigaban Zagwanni a Ghana, Muhammad Ben Banda

Tue, 27 Sep 2022 Source: www.bbc.com

Ministan ma'aikatar cigaban Zangwanni a kasar Ghana, Muhammad Ben Banda ya ce matsalar rashin ilimi ce take janyo koma-baya a yankunan.

Ya bayyana haka ne a hira da BBC hausa.

"Al'ummar da ke Zangwanni sun kai kaso 20 na mutanen kasar Ghana amma sakamakon rashin ilimi ya sa ba a jin su," in ji shi.

Sai dai kuma Muhammad Ben Banda ya ce kafa ma'aikatar zai ba shi damar magance matsalar wadda ya ce ita ce ta farko da ma'aikatar za ta fi mayar da kai.

Kusan kowane gari a kasar Ghana akwai Zango na Hausawa akalla guda daya.

Source: www.bbc.com
Related Articles: