0
Menu
News

Nijar: Yadda shaye-shaye tsakanin matasa ke neman zama ruwan dare a Maradi

 124125553 822fc381 74bf 428b A80a 6929b35ee1c6 Wasu matasa tare da kayan maye

Tue, 12 Apr 2022 Source: www.bbc.com

A jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar, matasa sun koka da yadda shaye-shaye ke neman zama ruwan-dare a tsakaninsu.

Matasan sun ce hakan dai na da nasaba da tabarbarewar tarbiyya da kuma sakaci na iyaye.

Cikin wata tattaunawa da wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou, ta yi da wasu matasa biyu a jihar, sun shaida mata cewa, a yanzu matsalar shaye-shaye tsakanin matasa ta yi yawa a jihar.

Daya daga cikin matasan mai suna Abdurrahman, ya ce a yanzu yaro ma sai yaje makaranta har lokacin tasowa ya yi bai dawo gida ba, amma idan ya dawo wasu iyayen basa tambayar inda ya tsaya.

Ya ce," Wani lokacin ma iyaye na ganin dansu da abokan da ba su yarda da su ba, amma ba sa iya yi musu magana."

Matashin ya ce, a da idan iyaye suka ga dansu da abokin da ba su san shi ba sai sun tambayi daga ina yake, kuma dan wanene, amma iyaye a yanzu ba ruwansu.

Abdurrahman, ya ce a gaskiya yanzu akwai sakaci a wajen iyaye wajen tabarbarewar tarbiyyar 'ya'yansu.

Shi kuwa daya matashin mai suna Aminu, cewa ya yi matsalar shaye-shayen ma har da dalibai, domin wasu yaran kafin su shiga aji, sai sun sha.

Ya ce," Akwai mahadar da matasa ke zama suna shaye-shaye a cikin unguwanni, kuma iyaye ba sa lura, sai ka ga yara sun fita sun kai wani lokaci ba su dawo gida ba."

Abdurrahman, kuwa ya ce, tabbas mahadar da matasa ke zama wato majalisa, na taimakawa wajen koya wa matasa shaye-shaye, saboda ko da mutum bai sha, yau da gobe ana sha a gabansa, wata rana sai shi ma ya yi sha'awa har ya fara.

Ya ce," A makaranta ma wani lokaci har da malamai ake haduwa taba shaye-shaye, misali idan malami ya dan zuki sigari sai ya mika wa dalibi, ko kuma dalibin idan ya sha shi ma sai ya mika wa malamin."

Matashin ya ce "A yanzu sai ka ga malami da dalibi sun zama abokai, ba wani abu ya hada ba kuma illa shaye-shaye."

Matasan biyu dai sun ce, a yanzu shaye-shayen ba wai maza ne kadai ke yi ba, har da mata.

Su ka ce, za ka ga mata na shan shisha da sirof (syrup) da dai sauransu.

Daga karshe, matasan sun yi kira ga iyaye da su rinka sanya idanu a kan inda 'ya'yansu ke zuwa, da su wa suke tare da su, da dai sauransu.

Kazalika matasan, sun ja hankalin 'yan uwansu matasa inda suka ce ya kamata su sani cewa su ne manyan gobe, idan har suka bata rayuwarsu tun yanzu, na kasansu ma abin da suke yi za su koya.

Don haka ya kamata su rinka sara suna duban bakin gatari idan za su yi abu, su tuna suna da kanne, in ji matasan.

Karin bayani

Ba a Jamhuriyar Nijar ne kadai ake fama da matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa ba, ko a Najeriya ma akwai wannan matsalar.

Matasa mata da maza na shan kwayoyi ko abubuwan da suke gusar musu da hankali.

Kuma ana danganta wannan matsalar a Najeriyar ma da sakacin iyaye.

Gwamnatoci kasashe da na jihohin a wasu kasashen na iya bakin kokarinsu wajen dakile matsalar shaye-shaye musamman a tsakanin matasa.

To amma babban kalubalen da ake fuskanta a yaki da wannna dabi'a shi ne yadda masu shan kayan mayen ke samun kayan hadin cikin sauki.

Masana dai sun ce idan ba a gagguta daukar matakin dakile wannan dabi`a ba, to a karshe za a samar da wata al`umma marar kan-gado.

Source: www.bbc.com
Related Articles: