0
Menu
News

Rashawa: EFCC ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan Najeriya

 124795095 Mediaitem124795093 Hukumar EFCC ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

Wed, 18 May 2022 Source: www.bbc.com

Hukumar da ke yaƙi da yiwa tattalin arziki ta'annati ta EFCC a Najeriya ta kama tsohuwar Shugabar majalisar wakilan ƙasar wato Patricia Etteh.

Jaridun cikin gida sun ruwaito cewa EFCC ta yi awon gaba da Ms Etteh ne a jiya Talata kan zargin almundahanar kuɗaɗe a ma'aikatar raya yankin Neja Delta wato NDDC da yawansu ya kai naira miliyan 287.

Wata majiyar EFCCn ta fada wa jaridar Punch cewa Ms Etteh ta karbi naira miliyan 130 daga kamfanin Phil Jin Project Limited da NDDC ta bai wa kwangilar naira miliyan 240 a 2011.

Akan haka a yanzu EFCCn ta neme ta tayi bayanin shigar kudin asusunta amma ta gaza fadar komai akai.

''Etteh ba darakta bace ko yar kwangila, saboda haka me ya kai wannan kudi asusunta. Akan haka muke bukatar ta yi bayani kuma kawo yanzu bata yi ba.'' Inji majiyar.

An zabi Patricia Etteh a matsayin Shugabar majalisa a 2007, to amma ta yi murabus ne bayan 'yan watanni bisa zargin karkatar da wasu kuɗaɗe.

'Yan majalisa a lokacin sun yi barazanar tsige ta daga mukamin Shugabar Majalisar kafin ta yanke shawarar sauka da kanta.

A wancan lokacin ana zarginta da ware wasu makudan kuɗaɗe don bada kwangilar gyaran gidan da aka tanadar wa kakakin majalisa.

Ita ce mace ta farko a Najeriya da ta taba jagorantar majalisar a tarihi.

Kamen nata na zuwa ne kwana ɗaya bayan da EFCCn ta cafke Akanta Janar na ƙasar Ahmed Idris, bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan 80.

EFCC ta ce ta kama shine bayan ya ki amsa gayyatar da tayi masa don amsa tambayoyi.

Wasu 'yan Najeriya sun rika cece-kuce kan kama Akanta Janar din da zargin wawushe biliyoyin, la'akari da cewa yana rike da babbar kujera a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ke ikirarin yaƙi da cin hanci da rashawa.

Source: www.bbc.com
Related Articles: