Menu

Abin da Buhari, Ahmad Lawan da Gbajabiamila suka tattauna

 117755389 Mediaitem117755388 Buhari tare da Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmad Lawan

Tue, 30 Mar 2021 Source: BBC

Rahotanni daga Najeriya na cewa akwai yiwuwar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari zai gabatar da ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi domin sayen allurar riga-kafin cutar korona da kuma makamai.

Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana wa manema labarai hakan bayan sun kammala ganawar sirri shi da Shugaba Buhari da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila a fadar shugaban ranar Litinin da dare.

Sanata Lawan ya ce: "Mun zo ne don ganawa da shugaban ƙasa da tattaunawa kan manyan abubuwan da suka shafi ƙasar. Ɗaya daga cikin abubuwan kuwa su ne batun samar da ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi."

Jaridar Punch ta ruwaito Sanata Lawan yana cewa: "Dukkan majalisun tarayyar biyu sun yi amanna cewa ya kamata a samar da ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi don sayen alluran rigakafin COVID-19 a Najeriya da kuma samar da kayan aikin da hukumomin tsaro ke buƙata a ƙasar."

Sai dai babu batun sayen waɗannan kayayyaki a kasafin kuɗi na 2021 da aka amince da shi a watan Disamban 2020.

Lawan ya jaddada cewa a halin yanzu manyan abubuwa biyu da ke ci wa Najeriya tuwo a ƙwarya su ne batun rashin tsaro da na annobar cutar korona.

Sanata Lawan ya yi ikirarin cewa harkar tsaro tana inganta a sannu a hankali a ƙasar.

"Ina son yin amfani da wannan damar na ce lamarin tsaro na inganta a hankali kuma na tabbata idan muka ƙara bai wa hukumomin tsaro abubuwan da suke buƙata, to za mu yi gaggawar ganin sakamakon mai kyau."

A taƙaice: Wasu abubuwan da Sanata Lawan ya faɗa

Gwamnati ba ta tunanin bai wa wani ɗan ƙasar da ya buƙaci dala miliyan 100 don gwajin samar da allurar

Majalisar dokoki za ta tabbatar da samar da kuɗaɗe don sayen makamai ga hukumomin tsaro

Kan batun Ƙudurin Dokar Man Fetur ta PIB, Lawan ya ce majalisun suna aiki tuƙuru a kansa

Najeriya za ta samar wa da masana kimiyyar ƙasar abubuwan buƙata don haɗa kai da sauran masana kimiyya daga sassan duniya don samar da allurar riga-kafin cutar korona.

Source: BBC