Menu

Ambaliyar ruwa a Australia: Hotunan mummunar ambaliyar ruwa mafi girma cikin shekara 50

 117656280 Gettyimages 1231817666 Rahotanni sun tabbatar da mummunar barna da ambaliyar ta haddasa

Mon, 22 Mar 2021 Source: BBC

Ambaliyar ruwan da aka dade ba a ga irinta ba cikin gwamman shekaru ta mamaye New South Wales, yayin da ake ci gaba da tafka ruwa kamar da bakin kwarya musamman a yankunan gabar teku na kasar Australia.

Tuni aka kwashe kusan mutane 18,000, saboda tumbatsar koguna da madatsun ruwan da ke babban birnin kasar Sydney da wasu yankunan da ke kusa da gabar teku.

Jami'ai sun ce za a ci gaba da fuskantar matsalar nan da makwanni masu zuwa, tare da bukatar mazauna yankunan su yi takatsantsan.

Rahotanni sun tabbatar da mummunar barna da ambaliyar ta haddasa.

Wasu sabbin ma'aurata sun ce a kan idanunsu ambaliyar ta share gidansu, a ranar da ya kamata ta zamo ta amarcinsu.

Source: BBC