BBC Hausa
Tue, 26 Apr 2022
Shugabannin gudanarwar kamfanin Tuwita sun amince a sayar wa attajirin nan Elon Musk kamfanin kan dala biliyan 44.
Mr Musk, wanda sanarwar sa ta son sayen kamfanin a makon jiya ta girgiza mutane, ya yi ikirarin zai iya bunkasa kamfanin ya ci gaba.Ya kuma sanar cewa zai kawo gagarumin sauyi a kamfanin — kama daga duba sahihanci abubuwan da ake wallafawa zuwa magance matsalar shafukan bogi.
Tun da fari shugbannin kamfanin sun ki amincewa da tayin Mr Musk, na siyan kamfanin, amma daga bisani shawara ta sauya bayan an kada kuri'a tsakanin masu hannayen jari a Tuwita.
Mr Musk dai shi ne attajiri mafi arziki a duniya, kuma kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana, an yi kiyasin arzikinsa da ya kai dala biliyan 273.6b, yawanci saboda hannayen-jarin da yake da su a
kamfanin Tesla mai kera mota da ke aiki da lantarki, wanda kuma shi ke gudanar da shi.
Sai kuma jarin da yake da shi na jagorantar kamfanin da ke zuwa sararin samaniya na SpaceX.
"'Yancin fadar albarkacin baki, shi ne kashin-bayan ingantacciyar dimukradiyya, kuma Tuwita duniya ce guda da ta kunshi mutane daban-daban, da kuma ke tattaunawa kan batutuwa da tafka muhawara kan makomar dan adam," in ji Mr Musk cikin sanarwar da ya fitar da ya bayyana kammala cinikin.
''Ina kuma son inganta Tuwita fiye da lokutan baya, ta hanyar inganta abin da ake yadawa, da kara hanyoyin inganta abubuwan da ake yadawa wanda zai kara sanya yadda tsakanin mau bibiyarmu, da magance labaran karya, da inganta abubuwan da suka shafi dan adam,'' in ji shi.
"Tuwita na da matukar amfani, ina farin-ciki da zakuwar aiki tare da kamfanin da masu bibiyar shafin domin kara bunkasa shi."
Shugabar gudanarwar Tuwita Bret Taylor, ta ce ta yi cikakken aiki domin ganin kamfanin ya duba bukatar Mr Musk.
Shugabannin gudanarwar kamfanin Tuwita sun amince a sayar wa attajirin nan Elon Musk kamfanin kan dala biliyan 44.
Source: BBC
Related Articles:
- CEOs lacking knowledge of AI, future of work trends face extinction in the business world - Report
- Elon Musk's Starlink operations are illegal in Ghana - NCA
- MoMo agents to limit cash withdrawals to GH¢1,000 per transaction from December 1
- Ghana to get 5G wireless data communication soon – NCA
- Ghana to get 5G wireless data communication next year – NCA
- Read all related articles