Menu

An kama jami'an tsaro bakwai masu 'taimaka wa ƴan fashi' a Zamfara

 118081182 4642c974 38b7 48e7 82f0 798f40aa7a65 Hoton sojojin Najeriya

Sat, 17 Apr 2021 Source: BBC

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kama wasu jami'an tsaro bakwai a jihar bisa zarginsu da taimaka wa 'yan fashi da makami a sassa daban-daban na jihar.

Gwamnatin ta sanar da haka ne a yayin wani taron manema labarai da ma'aikatun watsa labarai da harkokin tsaron na jihar suka gudanar a yau.

A sanarwar da gwamnatin ta raba wa manema labarai ta ce jami'an tsaron bakwai sun fuskanci tambayoyi kuma sun amsa laifukansu da suka hada da ƙyanƙyasa wa 'yan ta'adda bayanan sirri na soji, da samar musu makamai da kakin soji da sauran abubuwan da suke bukata.

Ta ce tuni aka miƙa wadannan jami'an tsaron bakwai ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar mataki a kansu.

"Daga cikinsu wanda aka kama yana kokarin miƙa wa wani riƙaƙƙen dan fashi mai suna Kabiru Bashiru albarusai 20 da ya sayar masa bayan ya biya shi kudi Naira dubu 100.

Ta ce na biyu kuwa wanda ya fito daga jihar Sakkwato, an kama shi yana kai wa 'yan fashin da uniform da sauran wasu abubuwan da sojoji ke amfani da su.

Yayin da aka kama shin, an samu da rigunan da harsashe bai ratsawa guda tara da kakin soja guda hudu da katin shaidar zama sojan Najeriya da sauransu.

Daga cikin wadanda aka kaman kuma har wayau akwai wani likita da aka samu da takalamin soja ƙafa 10 da garkuwar ƙwabri da kuma safar hannu seti biyar.

Sanarwar ta ce wannan kamen ya tabbatar da maganar da gwamnan jihar ya taɓa yi a baya cewa jama'a za su sha mamaki idan suka ji wadanda ke ɗaure wa ta'addacin gindi a jihar da ma maƙwabtanta.

Daga karshe sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta Zamfara na rokon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya cika alkawarin da ya yi na tura bataliya shida ta sojoji zuwa jihar, domin kawar da 'yan fashin da suka ƙi yarda da sulhu wadanda ke ci gaba da addabar al'umomin yankunan karkara a jihar.

Ko a ranar 23 ga watan Maris ma sai da rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta kama wani mutum da take zargin yana sama wa 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar Zamfara babura.

Rundunar ta kama mutumin ne a jihar Kano, inda bayanai suka ce yana sayen babura domin tafiya da su jihar ta Zamfara, ya kuma sayar wa yan bindigar a kan farashi mai yawan gaske.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yayin binciken da suka gudanar mutumin ya shaida musu cewa ya sayarwa da 'yan bindigar babura kusan 100, a kan sama da Naira dubu dari shida duk ɗaya.

Source: BBC