Menu

Auwal Daudawa: Abin da ya kamata ku sani game da kisan dan fashin daji

Zamfara  Naija Gwanmatin Zamfara ta tabbatar da mutuwar Auwalu Dauduwa, kasurgumin dan fashin dajin

Sun, 2 May 2021 Source: BBC

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce an kashe Auwalu Dauduwa, kasurgumin dan fashin dajin nan da ke da hannu wajen sace daliban sakandaren Kankara.

Kwamishinan Tsaron jihar, Abubakar Muhammad Dauran, ya shaida wa BBC cewa an kashe shugaban 'yan fashin dajin ne sakamakon rikicin da ya barke tsakaninsa da kungiyoyin 'yan fashi da ke hamayya da shi.

A cewarsa, an kashe dan fashin ne tare da wasu mabiyansa artabun da suka yi da wasu 'yan bindigar.

"A daren da ya gabata ne [Juma'a] muka samu labarin cewa an kashe Auwalun Daudawa...har ya dauki shanun wasu, kuma su ma wadannan 'yan fashi da ke yankin sun dauki alkawarin ajiye makamansu. To, a wannan ne hadari ya same shi aka kashe shi. Labarin da yake zuwo mana ke nan," in ji Kwamishina Dauran.

Ya kara da cewa har yanzu ba su kai ga tabatar da wadanda suka kashe dan fashin dajin ba, "sai dai muna yin bincike a kan lamarin."

Abubakar Dauran ya ce kodayake har yanzu ba su san inda gawar dan fashun dajin take ba, "amma ka san abu ne da ya kamata a yi bincike a gano ainihin takamaiman abin. Amma tabbatar ga labarin da ke zowa lallai an kashe shi din."

Ya ce akwai wadanda suka ga gawar dan fashin kuma ba shi kadai aka kashe ba, kodayake shi ma ya kashe wasu.

Kwamishinan ya ce Auwalun Daudawa ya je jihar ta Zamfara ne domin halartar daurin auren kannensa "don haka ya tafi da iyalinsa a kan cewa idan aka gama hidimar auren zai dawo, sai kuma ga shi a daren jiya wannan labari ya zo cewa wannan batu ya rutsa da shi."

Abubakar Dauran ya ce suna jiran jami'an tsaro domin su yi musu karin bayani kan kisa kasurgumin dan fashin dajin, yana mai cewa ba su samu wannan bayani ba ne "domin lamarin ya faru ne da tsakar dare."

A baya dai, Auwalu Daudawa ya ce ya tuba daga sana'ar fashin daji da kuma garkuwa da mutane.

Ya bayyana cewa shi ne ya shugabanci barayin dajin da suka sace 'yan makarantar sakandaren Kankara da ke jihar Katsina su fiye da 300 a watan Disambar 2020.

Satar daliban maza dai ta jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, kodayake daga bisani gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya shaida wa BBC cewa kungiyar Fulani ya Miyetti Allah ce ta jagoranci yin sulhu domin kubutar da su.

Source: BBC