0
MenuAfrica
BBC

Barcelona da Neymar sun sasanta a tsakaninsu

 119579803 Messineymar Messi (left) tare da Neymar Jnr

Tue, 27 Jul 2021 Source: www.bbc.com

Kungiyar Barcelona ta sanar ranar Litinin cewar ta sasanta da Neymar kan takaddamar da ke tsakaninta da wasan tawagar Brazil.

Dan kwallon Brazil da Barcelona sun samu takaddama a tsakaninsu, bayan da Barcelona ta sayar da Neymar ga Paris St-Germain a 2017.

Neymar ya yi zargin Barcelona ba ta biya shi alawus a kwantiragin da ya saka hannu a Oktobar 2016, kafin ya koma Paris St Germain kan Yuro miliyan 222 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya.

Hakan ne ya sa dan wasan Brazil ya kai Barcelona kara domin a biya shi Yuro miliyan 46.3, ita kuma kungiyar Barcelona ta yi karar shi da cewar ya karya ka'idar yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

Wani alkali a Barcelona ya yanke hukuncin a cikin watan Yuni cewar Neymar ya biya kungiyar Camp Nou Yuro miliyan 6.7.

Wasu kafar yada labarai a Sifaniya sun ce Neymar ya daukaka kara ya kuma kara maka Barcelona a kotu kan wani zargin na da ban.

Barcelona ta sanar da cewar ta yi sulhu da Neymar, an kuma kawo karshen tuhume- tuhumen da ke tsakaninsu a kotu yanzu komai ya wuce.

Source: www.bbc.com