Ƴan Najeriya sun karya kumallo da shugaban Hukumar da ke hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya a kafofin sada zumunta na intanet musamman a Twitter.
Buba Marwa, wanda aka naɗa shugaban NDLEA a watan Janairun 2021, yana shan yabo daga wurin ƴan Najeriya kan yadda yake bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
A ranar Lahadi ne Hukumar NDLEA ta ce ta kama hodar ibilis da kudinta ya kai naira biliyan takwas tare da kama babban mai safarar ƙwayoyi a filin jirgin saman Legas.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an kama babban mai safarar ƙwayoyin ne da ke zama a ƙasar Brazil a ranar Juma'a 14 ga watan Mayun 2021 lokacin da yake ƙoƙarin shigo da hodar iblis a Najeriya.
Hukumar ta kuma ce ta kwace dala dubu 24,500 da aka nemi a bayar a matsayin cin hanci domin hana gudanar da bincike, matakin da ya ja hankalin ƴan Najeriya.
NDLEA intercepts N8billion cocaine, arrests drug kingpin at Lagos airport
— NDLEA NIGERIA (@ndlea_nigeria) May 23, 2021
. Seizes $24,500 offered as bribe to compromise investigation pic.twitter.com/0PLyaOAAzr
Tun a ranar Lahadi ƴan Najeriya ke tsokaci game da hukumar NDLEA da kuma shugabanta Janar Buba Marwa a shafin Twitter.
Sunan Buba Marwa ya kasance ɗaya daga cikin wadanda aka fi yin tsokaci a Najeriya a ranar Litinin, inda ya samu tsokaci sama da 4,000 a Twitter kawai.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Yawancin ƴan Najeriya na tsokaci ne kan yadda kusan kullum hukumar NDLEA ke bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar ƙarƙashin shugabancin Buba Marwa.
Haka kuma suna fatan ɗorewar ƙoƙarin da hukumar ke yi na ci gaba da kama masu safarar miyagun ƙwayoyi.