0
MenuAfrica
BBC

Elon Musk ya sayi Twitter: Wanne sauyi za a samu a kamfanin?

Elon Musk In Black Elon Musk

Wed, 27 Apr 2022 Source: www.bbc.com

Elon Musk ya kulla yarjejeniyar sayen kamfanin Tuwita tare da yin alkawarin rage sa ido a kan shafin, wanda ya sa ake dasa ayar tambayar abin da wannan kudiri nasa ke nufi ga "masu mu'amala da fasahar sadarwar ta intanet."

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun nuna damuwa cewa rashin sa ido zai iya haifar da karuwar kalaman nuna kiyayya.

Su ma masu amfani da shafin Tuwita na tambayar ko hakan na nufin za a dawo da shafukan wasu da aka toshe.

Mutum mafi shahara da aka taba dakatar da shafinsa shi ne Donald Trump.

Bayan sanar da yarjejeniyar cinikin, kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun nuna matukar damuwa game da kalaman nuna kiyayya a shafin na Tuwita da kuma karfin da zai bai wa Mista Musk, wanda ke bayyana kansa a matsayin "mai tsananin goyon bayan 'yancin magana".

Ya kasance mai baki sosai a sukar da yake yi wa dokokin shafin na sa ido a kan abubuwan da ake wallafawa, yana mai cewa kamata ya yi Tuwita ya zama wani sahihin dandali na 'yancin magana.

A wata sanarwa bayan kammala yarjejeniyar cinikin, ya bayyana 'yancin fadar albarkacin baki a matsayin ''kashin-bayan ingantacciyar dimokuradiyya."

A wasu jerin kalamai a shafin Tuwita, kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce: "Mun damu da duk wasu matakai cewa Tuwita ka iya daukar matakin soke dokoki da manufofin da aka tsara don kare masu amfani da shafin.

"Abin da ba za mu so ba shi ne shafin Tuwita wanda runtse idonsa da gangan kan kalaman batanci ga masu amfani da shafin, musamman wadanda abin ya fi shafa da suka hada da mata, da mata-maza da dai sauransu."

Kamfanin Tuwita bai yi saurin mayar da martani kan bukatun da BBC ta mika masa game da maganganun ba.

Shin Trump zai sake dawowa?

An cire shafin Donald Trump baki daya a shekarar da ta gabata a daidai lokacin boren 6 ga watan Janairu a ginin majalisar dokoki a Washington.

Amma ko da an sake dawo masa da shafinsa na Tuwita da aka toshe, Mista Trump ya ce ba zai dawo ya cigaba da amfani da Tuwita ba, a maimakon haka zai koma amfani da na shi dandalin na Truth Social.

"Ba zan koma Tuwita ba, zan cigaba da amfani da Truth," Mista Trump ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News.

Ya kuma kara da cewa ya yi amanna Mista Musk, wanda ya kira a matsayin "mutumin kirki" zai "kawo cigaba" ga dandalin.

Wakilan Mista Trump basu mayar da martani ga bukatar da BBC ta mika musu ba.

Ming-Chi Kuo, wani mai sharhi kan al'amuran fasahar zamani a wani kamfanin TF International Securities, ya shaida wa BBC cewa Mista Trump zai iya yanke shawarar sake dawowa dandalin idan zai sake tsayawa takarar shugaban kasa ne shekarar 2024.

Har yanzu Twitter shi ne zafi mafi kyau a gare shi na yin maganganu, muddin Tuwita ta shirya sake dawo da shafinsa," Mista Kuo ya bayyana.

"Ba abu mai sauki bane ka kafa wani dandali mai yawan mabiya irin Tuwita kafin zaben shugaban kasa mai zuwa."

Shin mutane za su bar Tuwita?

Mista Musk ya ce yana fatan cewa manyan masu sukar lamirinsa za su cigaba da kasancewa a dandalin "saboda hakan shi ne ma'anar 'yancin magana."

Amma kuma wasu masu amfani da dandalin sun yi barazanar ficewa daga Tuwita, a yayin da tuni wasu suka fice.

Wata 'yar wasan kwaikwayo ta kasar Birtaniya Jameela Jamil, wacce aka fi sanin ta a rawar da ta ke takawa a wasan kwaikwayon talabijin mai dogon zango da ake kira The Good Place, ta bayyana cewa tana da yakinin cewa dandalin "zai kara zama wuri marar bin doka, da tsana, da nuna kiyayya ga wadanda ba 'yan kasa daya ba, da girman kai, da nuna kin jinin mata.

"Ina son wannan ya kasance rubutuna na karshe a Twitter," Mis Jamil da shaida wa miliyoyin mabiyanta.

Source: www.bbc.com
Related Articles: