0
MenuAfrica
BBC

Fernando Torres: Atletico Madrid ta bai wa tsohon dan wasanta kocin matasa

 119580338 Fernandotorres Fernando Torres, tsohon dan wasan Atletico da tawagar Sifaniya

Tue, 27 Jul 2021 Source: www.bbc.com

Atletico Madrid ta nada tsohon zakakurin dan wasanta, Fernando Torres a matsayin sabon kocin matasan kungiyar.

A kakar da ta wuce Torres ya yi aiki tare da karamar kungiyat Atletico a matakin mataimakin koci, wanda yanzu zai ja ragamar kakar da za a fata ta 2021-22.

Torres ya sanar a kafarsa ta sada zumunta a Twitter "Ina alfahari da murna da na koma giga. Wannan kalubale ne babba a gabana, zan yi iya kokari na don ci gaba da bautawa kungiyar nan,''

Mai shekara 37, wanda ya ci wa Atletico kwallo 121 a wasa karo biyu da ya yi wa kungiyar, wanda ya taka leda a Liverpool da Chelse zai yi aiki tare da dan uwan kyaftin Koke Resurrecion mai suna Borja, wanda zai ja ragamar matasa 'yan kasa da shekara 15.

Shi kuwa Fabio Futre dan gidan tsohon dan kwallon tawagar Portugal da Atletico, Paulo, shine zai horar da matasan kungiyar 'yan kasa da shekara 11.

Source: www.bbc.com