Menu

Fulani makiyaya sun ce har yanzu suna fuskantar tashin hankali a kudancin Najeriya

 117828962 B52d63f4 D327 41d7 B3f2 83684f13f745 Fulani makiyaya sun shiga cikin wani hali na kaka-ni-kayi a wasu jihohin kudun kasa

Sat, 3 Apr 2021 Source: BBC

Duk da alamun lafawar rikice-rikicen da Fulani makiyaya ke fuskanta a yankin kudu maso yammacin Najeriya, makiyayan da ke zaune a jihar Oyo sun ce da sauran rina a kaba.

Sun ce kawo yanzu suna ci gaba da zama cikin rashin kwanciyar hankali sanadin hare-haren da suka ce ana kai masu.

Sun kuma ce ana karkashe su tare da da dabbobinsu.

Shugaban reshen jihar Oyon na kungiyar Fulani makiyaya ta ''Gan Allah'', Yusuf Haruna ya shaida wa BBC cewa tashin hankalin ya tarwatsasu kuma ya yi ikirarin cewa mahukunta sun zura ido, ba su yin komai.

"Asarar da muka tafka ba za ta lissafu ba, don na biliyoyin naira ne muka yi asara banda rayukan mutane da dabbobi", a cewar Yusuf Haruna.

Ya kuma yi zargin cewa an kashe mu su mutane da dabbobi a kananan hukumomi uku da ke jihar Oyo.

Malam Haruna ya yi kira ga gwamnatin Najeriya a kan ta taimaka musu domin rage radadin asarar da suka yi.

Fulani makiyaya sun shiga cikin wani hali na kaka-ni-kayi a wasu jihohi da ke kudancin Najeriya tun bayan da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya debar wa maikiyaya wa'adi a kan su fice daga jiharsa.

Haka kuma wani dan bangar Yarbawa Cif Sunday Adeyamo wanda aka fi sani da Igboho ya umarci Fulani makiyaya a kan su bar jihar ta Oyo a kan zargin suna da hannu a satar mutane domin karbar kudin fansa.

Sai dai zargi ne da Fulani makiyaya suka musanta suna masu cewa kora da hali ne ake so a yi musu daga yankin na kudu maso yammacin Najeriya.

Source: BBC