Masu binciken laifukan cin hanci d rashawa a Najeriya na neman surukin Shugaban kasar mai suna Gimba Yau Kumo ruwa a jallo.
Hukuma Mai zaman kanta da ke yaki da miyagun halaye ta Najeriya ICPC ce ta wallafa sakon neman shi kan wata badakkalar kudaden mallakar gidaje da aka wawushe da darajarsu ta zarce dala miliyan 65.
Kumo shi ne tsohon shugaban gudanarwa na bankin Federal Mortgage Bank of Nigeria mai samar wa al'umomin kasar basusukan mallakar muhallai na cikin jerin mutane biyun da hukumar ICPC ta wallafa sunayensu da hotunansu a shafinta na intanet.
Sakon da aka wallafa tare da hotuna, wanda kakakin hukumar Azuka Ogugua ya sanya wa hannu a shafin hukumar na intanet ta ICPC na cewa:
"Mutanen da hotunansu mu ka wallafa a sama, Mista Tarry Ruffus, Mista Gimba Yau Kumo da Mista Bola Ogunsola sun kasance na wadanda mu ke NEMA...kan wata badakkala da ta shafi wawushe asusun ajiya na kasa kan mallakar muhallai da kuma karkatar da$65m".
Sakon ya kara da cewa duk mutumin da ke da wasu bayanai da za su taimaka a kama wadanda ke da hannu kan wannan badakklalar na iya sanar da babban ofishin hukumar ICPC a Abuja da rassanta na jihohi da kuma dukkan ofisoshin 'yan sandan Najeriya.
A shekarar 2016 ne dai Gimba Yau Kumo ya auri 'yar shugaba Muhammadu Buhari ta biyu mai suna Fatima.
Sai dai kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kasa samun mutum ukun domin su kare kansu, kuma kakakin shugaban Najeriya ya tabbatar da ana gudanar a bincike kan surukin na shi.
A watan Afrilu, wani kwamitin majalisar dattawan Najeriya ya gayyaci Mista Kumo domin ya bayyana dalilansa na ya bayar da wata kwangilar da ya ce ba a bi ka'aida ba wajen bayar da ita ba yayin da yake aiki a bankin, inji wani rahoto na jaridar Premium Times.
Shugaba Buhari wanda ya ke kan karagar mulki a karo na biyu, ya dade yana alkawarin yakar cin hanci da rashawa da ya yi wa Najeriya katutu.