0
MenuAfrica
BBC

Hari kan ayarin motocin Buhari: 'Yan bindiga sun raina gwamnatin shugaban Najeriya'

 125808560 D4d7c49e 3833 4ab3 9861 300790c201f7 Shugaba Muhammadu Buahri

Fri, 8 Jul 2022 Source: www.bbc.com

Wani hari da `yan bindiga suka kai kan ayarin motocin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ja hankalin 'yan kasar da masana harkokin tsaro, waɗanda ke cewa alama ce da ke nuna yadda lamarin tsaro ke kara taɓarɓarewa a kasar.

A ranar Talata da dare ne ƴan bindigar suka far ma ayarin a kan hanyarsa ta zuwa birnin Daura da ke jihar Katsina inda aka kai harin a kusa da garin Dutsinma na jihar.

Wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar ta ce an kai harin ne kan ayarin motoci dauke da jami'an da ke wa shugaban hidima yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Daura gabanin bikin Babbar Sallah.Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ba ya cikin ayarin motocin.

Yadda ƴan bindigar suka far wa ayarin shugaban kasar gaba-gadi, da wasu hare-hare da suka kai kan jami`an tsaro, ciki har da kisan da suka yi wa wani kwamandan ƴan sanda mai mukamin mataimakin kwamishina a Jihar Katsina, duka a ranar Talata, ya nuna yadda ƴan bindigar ke rawar gaban hantsi ba tare da an kwaɓe su ba.

Haka kuma da wani kwanton-ɓauna da ƴan bindigar suka yi wa sojoji a Jihar Neja, inda aƙalla aka kashe mutum talatin yayin da suka kai ɗauki bayan `yan bindigar sun kai farmaki kan wata mahakar ma`adinai a makon jiya, a cewar masana, manuniya ce ga yadda ƴan bindigar suke cin karensu ba babbaka.

Masanan dai na ganin ƴan bindigar suna yin haka ne saboda ba sa shakkar wani abu zai iya biyo baya lamarin da ke nuna cewa sun raina gwamnatin kasar.

Dakta Kabiru Adamu, masanin tsaro ne a Najeriya, kuma ya bayyana wa BBC cewa ga dukkan alamu ko jami`an tsaro sun yi watsi da wasu dabarunsu na yaki da `yan ta`adda ko kuma watakila wasu ma ba su fahimci logar aiki da dabarun ba, musamman ma tattara bayanan sirri da sa ido ko kasancewa a ankare a kowane lokaci.

"Waɗannan maharan a baya sun kai hare-hare, sun yi nasara kuma kusan babu wani sakamako na dangane da mataki wanda za a ce gwamnatin ta ɗauka har ya kai ga shafarsu," in ji Malam Kabiru Adamu.

Malam Kabiru Adamu ya bayyana cewa akwai hare-hare da dama da kuma nasarorin da ƴan bindiga suka samu waɗanda babu matakin da aka ɗauka dangane da hakan.

Malam Kabiru ya kuma bayyana cewa akwai rauni da jami'an tsaro suke da shi ta bangaren tattara bayanai da sa ido.

"Duk lokacin da ake harka irin wannan ta tsaro, ya kamata, ya kamata ka sa ido a kan shi abin da ka tura ɗin ya yi maka aiki wanda daga nesa ɗin za ka iya ganin shi abin da ka tura ɗin ko da wani abu ya so ya kai masa hari za ka iya ɗaukar mataki domin ka kare shi," in ji Malam Kabiru.

Me jama'a ke cewa kan harin da aka kai wa ayarin Shugaba Buhari?

Muhammad Bin Muhammad a shafin Facebook ya bayyana cewa ya yi addu'ar Allah kiyaye faruwar wannan lamari a gaba kuma ya ce wannan hannunka mai sanda ne ga shugaba Buhari.

Babangida Yunusa shi ma addu'a ya yi inda ya roƙi Allah ya kawo sauƙin wannan bala'i inda ya ce idan ƴan bindiga suka ci gaba da kai wa shugabanni hari za su ɗauki lamarin da gaske su yi maganion abin.

Shi ma Mustapha Abdullahi cewa ya yi akwai ƙalubale gaban shugaban Najeriya inda ya ce ya kamata a ce tun kafdin waɗannan mahara su yi ƙarfi an daƙile su.

Source: www.bbc.com
Related Articles: