An haifi Malam Yahaya Jibril wanda aka fi sani da Malam mai Tauhidi a garin Bauchi a wani kauye da ake kira Bigidam a ranar 1 ga watan Fabirairun 1967.
Kamar dai mafiya yawan malamai, shi ma Malam Mai Tauhidi ya fara karatunsa ne daga gida a gaban mahaifinsa Malam Jibril, inda ya samu karatun al-Kur'ani mai girma.
Bayan nan mahaifinsa ya tura shi wurin malamai daban-daban wasu a Bauchi wasu a wajen Jihar kamar su Kano domin ci gaba da karatu irin na addini.
Daga baya dai ya koma Bauchi da zama. A wasu lokutan yakan fita ya tafi gururuwa irin su Zaria domin dai ci gaba da neman ilimi, wanda a cewarsa ba a girma da shi.
'Na fara ne da yi wa mutane addu'a'
Malam Mai Tauhidi ya ce kai tsaye bai fara karantarwa ba, a baya 'addu'a muke yi wa mutane idan wani abu ya faru a kasar.
"Mukan tara almajirai a yi saukar Ƙur'ani a roki Ubangiji neman mafita," in ji Malam Yahaya.
Daga baya sai ya yi tunanin cewa mutanen kauyuka na bukatar a ilimantar da su, abin da ya sanya shi ya bar wa wasu manyan almajiransa makaranatar da yake koyarwa ya fara shiga kauyuka.
"Wannan aiki an dage ana gudanar da shi saboda yi wa addini hidima ne da ya kama malamai daga ko wacce jiha su dauki gabarar yi," Mai Tauhidi ya fada.
Me yasa matasa ke son tafsirinka?
Ko da aka yi wa Malam wannan tambayar sai ya yi murmushi ya ce "Wannan gaskiya ne a duk lokacin da muke yin karatu matasa na zuwa ba dan komi ba sai domin dalilai kamar haka.
"A mafi yawan lokuta mukan jefa raha da barkwanci a cikin koyarwarmu, kuma haka addini ya ce a rika yi a koyar cikin hikima da dabaru.
"Ina yawan yi wa matasanmu addu'a, kuma hakan yana da matukar tasiri a kansu, Allah ya shiryi matasanmu ya kare su ya basu abin yi da dai sauransu," in ji Malam.
A wasu lokutan yana yawan janyo su kusa da shi ya rika yi musu nasihar, ya ce ko mai shan "wiwi" baya kyama, yakan nuna masa cewa babu wani wanda ya zama gwamna ko shugaban kasa ta dalilin shan "wiwi".
Malam ya kan tunatar da matasa cewa sata ba abu ba ne mai kyau, babu wani wanda ya yi fice da ita ya zama kuma abin koyi a cikin al'umma.
"Mafi munin abin da za kuyi shi ne raina iyaye, kada ku raina iyayenku, ku yi musu biyayya, ku girmama na gaba da ku, haka zalika malamanku, kuma duka abin da zai iya samar da zaman lafiya a inda kuke shi ya kamata ku yi," a cewar Malam.
Abin farin ciki da ba za ka taba manatwa da shi ba
Malam ya ce akwai abubuwa da yawa da ba zai taba mantawa da su ba, amma wanda ya fi tsaya masa a rai shi ne, ranar da mahaifinsa ya ce Yahaya yau ka sauke al-Kur'ani mai girma.
Wannan rana a cewar malam ba zai taba mantawa da ita ba.
An tambayi Mai Tauhidi wani abin bacin rai da ba zai manta da shi ba, kamar dai na farin cikin, sai Malam ya ce, "ranar da aka wayi gari wani ya yi batanci ga Annabi Muhammad, a kullum na tuna abin yana dawo mani kamar sabo".
Wacce sura ce ta fi wahalar da Malam?
Ba a rasa wata sura ko aya da ke bai wa makarancin Ƙur'ani wahala ko kuma ta nuna gajiyawarsa a matsayin mu'ujizar al-Kur'ani, kamar yadda masana ke fada.
Mai Tauhidi ya ce "Suratul Balad" ce ta wahalar da shi yana yaro, kuma ya ci duka a kan surar.
Har zuwa yau idan ya tuna sai ya yi ta mamaki.
Ko da aka tambaye shi yana da "Kundi" kamar yadda wasu makaranta ke da shi, sai Malam ya ce a ganinsa babban kudi shi ne kiyaye Allah madaukakin Sarki.
Hadithi ya tabbata cewa "Idan ka kiyaye Allah shi ma zai kiyaye ka a duk inda kake, "Kasan ni gaddi ne na yankan shakku don haka na mallaki kundi da yawa an kuma ajiye su ne domin bacin rana.
Wani dan siyasa ya taba batan rai, sai da ya biyo ni har saudiyya ya ba ni hakuri, to kaji maganar kundin," in ji Malam.
Wanne abinci Malam ya fi so?
Malam ya fara da dariya, ya yi wa mai tambayar addu'a ya ce "na fi son tuwo ya dahu, da miyar kuka ko kuma kubewa danya".
Malam ya ce babban burinsa shi ne kasarsa ta zauna lafiya wadannan tashe tashen hankulan da ake yi su zo karshe, al'amura su koma yadda suke a baya.
Ta fuskar lahira kuma yadda kuma shi ne in cika da imani, wanda shi ne burin ko wanne mai rai a duniya.
Ya ya batun iyali?
"Yau shekarata 35 da auren fari amma sai a kwanan nan Allah ya fara ba ni haihuwa, na samu jinkirin haihuwa ina da mata uku da yara 10".