0
MenuAfrica
BBC

Kudurori uku da matsin lambar mata ya tilasta wa majalisar Najeriya sauya su

 123609048 Matanajeriya Yayin da wasu mata suka yi zanga-zanga a Abuja

Wed, 9 Mar 2022 Source: www.bbc.com

Majalisun dokokin Najeriya sun amince su sake duba wasu ƙudiri uku da suka shafi mata ciki har da ƙudirin da zai ba su kashi 35 cikin 100 na muƙaman siyasa, wanda 'yan majalisar suka ƙi amincewa da su tun farko.

Matakin na zuwa ne yayin da aka yi bikin Ranar Mata ta Duniya ranar Talata, inda a Najeriya ɗaruruwan mata suka gudanar da tattaki zuwa zauren majalisar a karo na biyu don matsa wa hukumomi lamba su samar da dokokin da za su taimaka musu.

A cewar Majalisar Wakilai, sun ƙi zartar da ƙudurorin ne sakamakon sun gaza samun ƙuri'un da suka dace yayin da ake kaɗa ƙuri'u kan ƙudurorin da za a sauya a Kundin Tsarin Mulkin Najeriyar na 1999 a makon da ya gabata.

"An sake mayar wa babban kwamiti ƙudirorin don sake duba su ranar Talata bisa amincewar Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila da kuma Majalisa," in ji majalisar.

'Yan majalisar sun yi watsi da ƙudiran ne duk da cewa Matar Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta je zauren majalisar da kanta lokacin da kwamatin gyaran kundin mulkin zai miƙa rahotonsa don tabbatar da cewa ƙudiriron sun samu shiga.

Hakan ya sa matan suka hana shiga da fita inda suka yi zaman dirshan a bakin ƙofar majalisar har sai da shugabannin majalisar suka rarrashe su.

An hangi mata 'yan majalisa na murna a ranar Talata na murna da sowa a zauren majalisar jim kaɗan bayan sanar da matakin sake duba buƙatun nasu.

Waɗanne ƙudurori ne?

"Wannan wani abin farin ciki ne a gare mu matan Najeriya da jin wannan labari cewa majalisa za ta sake dubawa, ba ma mu kaɗai ba har da na ƙasashen waje," kamar yadda 'yar Majalisar Wakilai Zainab Gimba ta shaida wa BBC Hausa.

"Wannan alama ce da ke nuna cewa haƙarmu za ta cimma ruwa kuma hakan ne ke ƙara mana ƙarfin gwiwa.

"Za mu ci gaba da bi muna wayar musu da kai cewa ba wai maganar mata ba ce kawai, mu ma wani ɓangare ne na al'umma."

Ƙudirorin su ne:

Bai wa majazensu damar zama ɗan ƙasa

Ɗaya daga cikin ƙudirorin shi ne wanda ya nemi a sauya tanadin kundin tsarin mulki game da mijin da 'yar Najeriya bke aure ɗan ƙasar waje idan yana so ya samu shaidar zama ɗan Najeriya.

Ƙudirin ya tanadi cewa duk wani ɗan ƙasar waje da ke auren wata 'yar Najeriya yana damar neman shaidar zama ɗan ƙasa.

Da ma tuni kundin tsarin mulki ya tanadi bai wa matar da ɗan Najeriya ke aure 'yar ƙasar waje damar zama 'yar ƙasa kai-tsaye.

Zama 'yar jihar mijinta

Wani ƙudirin da matan suka gabatar shi ne wanda ya nemi a bai wa mace damar zama cikakkiyar 'yar jihar da mijinta ya fito.

Ƙudirin ya nemi mace za ta zama 'yar jihar da aka haifi mijinta bayan shekara biyar da aure.

Muƙaman siyasa

Ƙudiri na uku shi ne wanda matan ke son a ba su kashi 35 cikin 100 na dukkan muƙamai a cikin jam'iybyun siyasar Najeriya.

Kazalika, ya buƙaci a tanadar wa mata kashi 35 cikin 100 na kujerun wakilci a majalisun siyasar ƙasar.

Ƙudurorin da 'yan majalisa suka amince da su

Yayin ƙuri'ar da suka kaɗa don gyaran kundin tsarin mulkin, ƴan majalisar sun jefa ƙuri'a kan batutuwa kusan 70 waɗanda aka amince da waɗanda ba a amince ba.

Waɗanda aka amince su nekamar haka:

 • Kafa ofishin babban akawun na ƙasa da kuma ofishin babban akawun gwamnatin Najeriya


 • Raba ofishin babban mai shigar da ƙara na ƙasa da na jiha daga na ministan shari'a da na kwamishinan shari'a


 • Bai wa ƙananan hukumomin Najeriya damar cin gashin kansu a ɓangaren gudanar da mulki da kuma bangaren sarrafa kudaden shiga


 • Amincewa da ƙudurin ba majalisun jihohi da bangaren shari'a cin gashin kansu ta bangaren kudaden da tsarin mulki ya ce a ware musu


 • Akwai tabbatar da ana bin sammacin da majalisa ke fitarwa akai-akai


 • Ƙaddamar da 'yan majalisar dattawa da 'yan majalisar wakilai


 • Shigar da tsarin aiki na bangaren shari'a cikin tsarin mulkin Najeriya


 • Daidaita shekarun yin ritaya da inganta damar karbar kudaden fensho ga ma'aikatan bangare shari'a


 • Amincewa da a rika zama na musamman a majalisa kafin a amince da korar duk wani jami'in shari'a
 • Kara wa wasu jami'an gwamnatin ikon aiwatar da wasu bukatun gwamnati (kamar ma'aikatan gidan yar da na sufurin jirgin sama da na sufurin jirgin kasa)


 • Samar da wani rumbun ajiyar bayanan al'umma wanda a ciki za a adana bayanan yatsusu da na fuskokinsu


 • Inganta tsarin samar da lantarki na bai daya a Najeriya


 • Raba bangaren shugaban kasa da na gwamna da ikon da suke da shi na wucin gadi na yin dokoki


 • A samar da wasu takaitattun kwanakin da a cikinsu za a mika wa majalisa sunayen mutanen da ake son nadawa ministoci ko kwamishinoni


 • A samar da wani tsari na lokacin da za a dauka kafin a gabatar da kudurin doka na kasafin kudi ga majalisa


 • A shigar da manyan jami'an majalisun Najeriya cikin majalisar tsaro ta kasa


 • An amince da a ba majalisun kasar ikon kiran shugaban kasa da gwamnoni su bayyana a gaban majalisun a kowane lokaci bukatar yin haka ta taso


 • Kafa majalisar tsaro a matakin jihohi


 • Samar da jadawalin lokacin yin kidayar al'ummar Najeriya


 • Shugaban kasa da gwamnoni za su rika gabatar da jawabai na shekara-shekara a gaban majalisun kasar
 • Sake tsara mambobin majalisar kasa


 • Ba duk mai sha'awa damar tsayawa takarar zabe ba tare da sai ya shiga inuwar wata jam'iyyar siyasa ba.


 • Ƙudurorin da ba a amince da su ba

 • An ƙi amincewa da kudurorin da ke neman daidaito tsakanin jinsuna


 • Ba a amince da kudurin ba 'yan najeriya da ke zaune a kasashen waje shiga zabuka ba


 • Ba a mince a fadada kariyar daga hukuntawa da bangaren gudanarwa ke da ita ba


 • An ki amincewa da tsarin nan na amincewa da dukkan kudurorin dokar da shugaban kasa ya yi watsi da su


 • Batun cire shugabannin majalisa


 • Shigar da dokar haraji kan kayayyaki masarufi cikin dokar da bangaren tarayya kawai ke iko da shi


 • An ki amincewa da bayyana abubuwan da za a iya cewa na muzgunawa ne ko na cin mutumci da wulakanci ga 'yan kasar.


 • Source: www.bbc.com