Menu

Man United ta takawa Man City burki a cin wasanni a jere

 117485479 Pepguardiolagetty Kocin Man City Pep Guardiola

Tue, 9 Mar 2021 Source: BBC

Manchester United ta yi nasarar doke Manchester City da ci 2-0 a wasan Premier League da suka fafata a Etihad ranar Lahadi.

Minti biyu da fara tamaula, United ta ci kwallo ta hannun Bruno Fernandes a bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuma fenariti na 92 a gasar Premier ta bana.

Kungiyar Old Trafford ta ci kwallo na biyu ne ta hannun Luke Shaw, bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu.

Kafin karawar ta hamayya City ta ci wasa 21 a jere a dukkan fafatawa, kuma na 28 da ba a samu nasara a kanta ba.

Rabon da a yi nasara a kan City tun ranar 21 ga watan Nuwamba, wanda Tottenham ta doke kungiyar ta Etihad da ci 2-0 a gasar Premier League.

Ita kuwa Manchester United ta buga wasa 22 a waje a jere ba tare da an doke ta ba a gasar Premier League,, ciki har 14 da ta lashe daga ciki.

City ta ci wasa 21 a jere a dukkan fafatawa tun bayan da ta tashi kunnen doki 1-1 da Wesr brom ranar 18 ga watan Disamba a gasar Premier League.

A wasa 21 da ta ci a jere har da karawa biyu a Caraboa da uku a FA Cup da cin wasan Champions League daya, sauran bajintar a Premier League ta yi.

Da wannan sakamakon City mai fatan lashe kofi hudu a bana, tana ta daya a kan teburi da maki 65, ita kuwa United tana ta biyu da tazarar maki 11 tsakaninta da City.

Source: BBC