BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Manjo Janar Farouk Yahaya: Buhari ya naɗa sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya

Farouk Yahya Nigeria Army Chief COAS Major General Manjo Janar Farouk Yahaya ne sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya

Thu, 27 May 2021 Source: BBC

Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya.

Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis.

Naɗin na zuwa ne kwana shida bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru mai jagorantar rundunar.

Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, da kuma wasu mutum 11 cikin har da janar-janar uku.

Source: BBC