0
MenuAfrica
BBC

Matan Somaliya sun yi bajen-kolin hotunan 'ƙawance da lalle da rayuwar wajen aiki'

 123609042 Fc85550a Ada8 4f24 B6e4 Cb91a47f4627 Cibiyar Al'adu ta Somaliya Saf ce ta ƙaddamar da bikin mai taken 'Through My Lens'

Wed, 9 Mar 2022 Source: www.bbc.com

An buɗe wani baje-koli a Mogadisu babban birnin Somaliya da ake nuna ayyukan wasu mata masu ɗaukar hoto takwas da ke aiki a birnin.

Cibiyar Al'adu ta Somaliya Saf ce ta ƙaddamar da bikin mai taken 'Through My Lens'.

Ga dai wasu daga cikin ayyukan da aka baje-kolinsu a wajen bikin.

Deka Ali Hashi ta mayar da hankali ne a kan ilimi, inda ta ɗaɗɗauki hotunan ƴan mata a makarantar sakandare a gundumar Hodan da ke Mogadishu.

Hoton nan na ƙasa wanda aka dauka a bara, an sa masa suna "Manyan ƙawaye."

Ita ma Nuura Mohamoud Abdirahman ta nuna muhimmancin ƙawance a hotunan da ta tattara.

Ta ce ba a cika bai wa mata goyon bayan yin ƙawance ba.

A wannan hoton da ke nuna hannayen mutane sun tare kan wata, cibiyar Saf ta ce yana nuna wata budurwa ce da ke cikin farin cikin ganin mata 'yan uwanta sun sanya hannayen tallafarta da nuna mata ƙauna.

Negad Mohamoud Abdirahman kuwa ta mayar da hankali ne wajen batun yadda ake bai wa man bilicin muhimmanci a zamanin nan na amfani da Instagram.

Wannan hoton na ƙasa an yi masa take da: Wata mata ƴar Somaliya na shafa man bilicin da ka iya jawo cutar kansa.

Falastin Khalif Yuusuf ta yi nata ayyukan ne kan yadda mata suka zama masu ƙwazo da ƙirƙira ta fannin sana'o;i, inda a bara ta ɗauki wani hoto na wani shagon gyaran kai da jiki na mata da ke koya wa mata yadda ake yin zanen ƙunshi.

A Somaliya, akan yi wa amare ƙunshi a hannayensu a lokacin biki, amma ita kuwa Mohamed Warsame sai ta yi duba kan illar yi wa yara mata auren wuri.

A wannan hoton na ƙasa sai ta nuna halin takaicin da yara mata kan shiga idan suka ji labarin cewa za a yi musu auren wuri.

Sagal Ali Ibrahim ta yi duba ne kan yadda mata ke faɗi-tashin neman na kansu a wuraren sana'arsu a kasuwa.

Hoton nan na ƙasa da aka ɗauka a bara, an yi masa take da "Wata mace na sayar da tumatur a Kasuwar Suuqa Beerta".

Ita kuwa Hafsa Jaamac Shire abin da ya fi birge ta shi ne shigar matan Somaliya cikin harkokin siyasa wacce maza suka mamaye.

Wannan hoton na ƙasa na wata ƴar uwarta ce wacce ƴar majalisa ce - an ɗauki hoton ne tana cikin wasu sabgoginta na yau da kullum ba na ofis ba.

Yayin da ita kuma Maryam Ahmed Warsame ta fi so ta nuna rayuwar mata a wuraren ayyukansu da al'ummar Somaliya suke ganin maza sun mamaye komai.

A wannan hoton na ƙasa, an nuna mata ƴan jarida ne a ɗakin yaɗa labarai da aka ɗauka a bara.

Source: www.bbc.com