BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Salim Ja'afar Mahmud Adam: 'Abin da mahaifina Sheikh Ja'afar ya gaya mini kafin ya rasu'

 118066777 P09drlqp Salim Mahmud Adam, Dan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Fri, 16 Apr 2021 Source: BBC

Dan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, ya bayyana shakuwar da ke tsakaninsa da mahaifinsa kafin a kashe shi shekaru 14 da suka gabata.

A hirarsa da BBC, Salim Mahmud Adam ya bayyana irin halayen mahaifinsa da kuma rawar da ya taka wajen tabbatar da cewa zuriyarsa ta kasance mai cike da hakuri da tsoron Allah.

Ya ce mahaifinsu ya yi tsayuwar daka domin ganin sun samu ilimi, kasancewar sun taso a gidan karatu wanda haka suka ga mahaifinsu yana yi musamman karatun Alkur'ani mai girma.

A cewarsa kasancewa Sheikh Ja'afar ba shi da isasshen lokacin da zai koyar da su karatu da kan shi saboda Da'awa da yake yi, amma ya yi kokarin ganin sun samu ingantaccen ilimi musamman abin da ya shafi karatun Alkur'ani.

Salim ya yi karin bayani kan abin da ya faru a ranar da aka kashe mahaifinsa, yana mai cewa "dama mutuwa kowa ya san dole wata rana zai tafi, da zarar lokacinka ya yi babu makawa za ka tafi.

Amma rasuwa irin wannan a lokacin, hakikanin gaskiya mun shiga wani yanayi na tashin hankali da damuwa, musammam mutuwa ce da ta zo kwatsam a wannan lokacin."

A cewarsa: "A cikin 'ya'yansa ni ne na karshe da ya yi magana da shi gabanin mutuwarsa, domin ya tashe ni zuwa masallaci sallar Asuba kafin na kai ga masallacin abin da ya faru ya faru.

"Duk da cewa ina da karancin shekaru a lokacin, ban mallaki hankalina ba, amma gaskiya a wannan ranar ba karamin tashin hankalin na shiga ba," in ji Salim.

Dan fitaccen malamin ya kara da cewa kasancewar mahaifinsu mutum ne mai aminai da 'yan uwa na gari, bayan rasuwarsa sun yi tsayin daka wajen bai wa iyalinsa taimakon da ya dace, musamman fannin ilimi da bukatun yau da kullum.

"Daya daga cikin abubuwan da ke faranta min rai, shi ne duk lokacin da na ji karatun malam ko ana sauraren karatun ko ganin bidiyon wa'azinsa. Da yadda mutane suke yi masa addu'a, da fatan alkhairi, wannan na sanya ni farin ciki da jin dadi," a cewarsa.

''A duk lokacin da na ga bidiyon wa'azin malam, kewar sa kan lullube ni, irin kewar mahaifi musamman a yanzu da ya kai shekarun girma suka same ni, ina matukar bukatar mahaifina ta fannin shawarwari na abubuwan da suka shafi mu'amalar yau da gobe,'' a cewar Salim.

Ya kara da cewa: "Alhamdulillahi, yawancin duk lokacin da na kalli wa'azinsa na kan samu wasu abubuwa da za su taimaka min da wani abu da zai amfane ni na yau da gobe. Malam ya yi kokarin nuna mana mu bi rayuwa a hankali, da girmama na gaba damu."

Duk da cewa a lokacin da aka kashe Sheikh Ja'far Mahmud Adam, Salim yana karami amma ya ce zai iya tuna wasu daga cikin abubuwan da suke faranta wa mahaifinsa rai.

"Duk da kankantar shekaruna, amma zan iya tuna daya daga cikin abin da ke farantawa Malam rai, shi ne ya dawo gida ya zauna cikin iyalansa. A yi wasa a yi dariya, ya ji matsalolinmu, da tambayarmu abubuwn da muke bukata na rayuwa. Wannan na cikin abubuwan da idan na tuna su na sanya ni farin ciki."

A ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 ne wadansu 'yan bindiga suka harbe Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, yayin da yake jagorantar Sallar Asuba a mallasaci da ke birnin Kano - wato a jajiberin zaben gwamnoni wanda aka yi a shekarar.

Wane ne Sheikh Ja'afar Adam?

  • An haife shi ne a ranar 12 ga watan Fabrairun shekarar 1961 a Daura jihar Katsina


  • Ya koma Kano don yin karatun allo yana da kimanin shekara hudu a duniya


  • Ya fara yin karatun addini ne a wurin mijin yayarsa


  • Ya haddace Al-Kur'ani a shekarar 1978


  • Ya fara karatun boko ne a shekarar 1990

  • Ya yi karatun addinin Musulunci a kasashen Saudiyya da Sudan, inda ya samu digiri na biyu.


  • Yana koma wa garin Maiduguri duk shekara don gudanar da tafsirin Al-Kur'ani a kowane watan azumin Ramadan




Source: BBC