0
MenuAfrica
BBC

Sojoji sun yi artabu da 'yan Boko-Haram da ke kwasar ganima a Damasak

Tue, 13 Apr 2021 Source: bbc.com

Sojoji sun yi artabu da 'yan ta'addan Boko-Haram/ ISWAP da ke kwasar ganima a Damasak a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Sojojin kasa tare da taimakon jiragen sama na rundunar sojin sama sun yi bata kashi da 'yan ta'addan Boko Haram a Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar na jihar Borno.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta tattaro cewa ana zargin wasu daga cikin yan ta'addan suna kan kwasar ganima yayin da suka afka wa rumbunan ajiyar kungiyoyin agaji na kasa da kasa a cikin motocinsu.

Wani jami'in leken asiri ya ce 'yan ta'adda sun zo a cikin manyan motocinsu suna kai hari kan rumbunan ajiyar kafin isowar jirgin sojan.

<

"Labari mai dadi shine cewa jirgin rundunar sojin sama ya kai mu su hari ta sama yayin da aka jibge sojojin kasa a wasu wurare masu muhimmanci suna musayar wuta", in ji majiyar.

A watan Maris daya gabata, jirage masu saukar ungulu sun kashe gomman mayakan ISWAP / Boko Haram a lokacin da suka kai hari a garin.

Source: bbc.com