Menu

Tsohon Gwamnan Legas ya ce har yanzu tattalin arzikin Najeriya yana da rauni

 117734414 44f07dbb Fee5 4b6d Bdc9 F669815950f6 Tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Bola Ahmad Tinubu

Mon, 29 Mar 2021 Source: BBC

Asiwaju Bola Tinubu wanda jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce har yanzu tattalin arzikin kasar yana da rauni duk da cewa kasar ta fice daga durkushewar tattalin arziki.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron tunawa da Sardaunan Sokoto, marigayi Sir Ahmadu Bello da aka yi a Kaduna ranar Asabar.

Hukumar kididdiga ta kasar a watan Fabarairun da ya gabata ta sanar cewa arzikin da kasar ta ke samar wa cikin gida ya karu da kashi 0.11 a karshen wata hudu na shekarar 2020.

A cewar hukumar ta NBS, ci gaban ya nuna cewa tattalin arzikin kasar ya farfado daga koma bayan da ya samu.

Sai dai a jawabin da ya yi lokacin da ya gabatar da wata takarda mai taken "Rage yawan kudin da ake kashewa kan shugabanci don ci gaban kasa da matasa a arewacin Najeriya bayan annobar korona", Tinubu ya ce har yanzu da sauran rina a kaba.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya ce duk da matakan da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka, kawo yanzu tattalin arziki kasar yana da rauni saboda akwai mutane da dama da ba su da ayyukan yi.

"Ya yinda kasar ta ke fuskantar kalubale sai aka samu bullar annobar korona wadda ta shafi tattalin arzikin duniya baki daya ciki har da Najeriya" in ji shi.

Sai dai ya jadadda bukatar ganin cewa an zaftare yawan kudaden da ake kashe wa jami'an gwamnati domin 'yan Najerya su amfana daga tattalin arzikin kasarsu".

Da yake Magana game da karuwar tashin hankali a Najeriya, Tinubu ya ce kasar ba za ta iya shawo kan matsalar ma su aikata miyagun laifuka ba, da kuma matasa ma su tada husuma idan ba ta samar mu su da guraben ayyukan yi ba.

Source: BBC