0
MenuAfrica
BBC

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tsallake rijiya da baya

 124070883 Af29954b 2b3a 4d04 851b 72822627c3e0 Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Thu, 7 Apr 2022 Source: www.bbc.com

Rahotanni daga Najeriya na cewa ayarin motocin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sun yi hatsarin mota a Abuja.

Da yammacin ranar Laraba ne hadarin ya faru lokacin da wakili na musaman na kungiyar ECOWAS ya bar filin jirgin saman Nnamdi Azikwe domin zuwa gidansa da ke Abuja.

Hadarin ya kuma yi sanadin mutuwar wasu 'yan sandan biyu da ke tare da shi.

Rahotanni sun ce al'amarin ya faru ne da misalin karfe hudu na yammaci jiya a hanyar Bill Clinton Drive

Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Ikechukwu Eze a wata sanarwa da ya fitar ya ce Mista Jonathan ya nuna matukar bakin cikinsa kan mutuwar 'yan sandan.

An kuma garzaya da wasu 'yan sanda biyu da suka ji raunuka a hadarin .

Mista Eze ya shaida wa BBC cewa hatsarin bai shafi tsohon shugaban kasar ba, domin motar da ke dauke da 'yan sandan ce ta kauce hanya a lokacin da direban ya rasa yadda zai yi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 'yan sandan biyu.

Rahotannin sun kuma ce Mista Jonathan ya tsira ba tare da kwarzane ba

Source: www.bbc.com
Related Articles: