Tsohon gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya Willie Obiano
Tsohon gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya Willie Obiano shi ne na baya-bayan nan cikin gwamnonin kasar da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFCC ta kama bayan da suka rasa kariyar da tsarin mulki ya ba su yayin da suke rike da mukaman gwamnoni.
A 'yan shekarun nan hukumar ta kama akalla gwamnonin Najeriya 30 kan tuhume-tuhume daban-daban kuma a lokuta daban-daban.
A yawancin lokuta laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa sun hada da karkatar da kudaden ayyuka da kudaden al'umma zuwa ga bukatu na kansu.
Kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, gwamnoni na da dumbin iko kuma su ne ke juya kasafin kudin jihohinsu, wanda har ya zarce na wasu kasashen Afirka yawa.
Manyan ƴan Najeriyar da EFCC za ta tuhuma a shekarar 2021 Domin kare martabar ofishinsu na gwamna, akwai wata doka da ke ba su kariya daga kamawa da gurfanawarwa a gaban shari'a.
Sashe na 308 na tsarin mulkin Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi masa gyara daga baya, ya ce:
"Ba tare da la'akari da wani abin da ya take tanade-tanaden wannan tsarin mulkin ba, kuma kamar yadda karamin sashe na (2) na wannan sashen ya samar, babu wata tuhuma ko wata shari'a da za a gudanar ko ko za a ci gaba da saurara kan mutumin da wannan sashen ya ambato yayin da wa'adisa na mulki ke gudana."
"Babu wata hukuma da ke da ikon kama dukkan mutumin da wannan sashe ya ambato ko ta tsare shi a kurkuku domin ta gudanar da wani aiki na shari'a ko ma wane irin aiki ne; kuma yana da kariya daga duk wata bukata ta shari'a da ke bukatar a gurfanar da wannan mutumin ko tilasta ma sa bayyana a gaban shari'a.
Saboda haka ne EFCC ba ta iya kama dukkan wani gwamna sai bayan ya saka daga mukaminsa, kuma bayan kariyar da tsarin mulki ya ba shi ta kare.
Sunayen tsofaffin gwamnonin da EFCC ta kama
Tun farkon Jamhuriya ta hudu a 1999 zuwa yanzu EFCC ta kama gwamnoni 30, tsohon gwamnan Anambra Willie Obiano ne na 31.
Willie Obiano
Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamna Obiano ranar Alhamis 17 ga watan Maris 2022.
An kama shi ne ranar da ya mika mulki ga sabon gwamnan jihar Charles Soludo.
Jami'an hukumar EFCC sun ce sun dade suna bincike kan tsohon gwamnan amma saboda kariyar da tsarin mulki ya ba shi ba su iya kama shi ba.
James Ibori
James Ibori wani tsohon gwamnan jihar Delta ce da ke kudancin Najeriya, inda ya shafe sheara takwas yana mulki (1999 zuwa 2007). An daure shi na tsawon shekara 13 a ne bayan da aka tuhume shi da zambar dalar Amurka kusan miliyan 77.
A gaban wata kotun South Crown Court ta Birtaniya, tsohon gwamnan ya yarda cewa ya aikata laifuka 10 cikin tuhume-tuhumen da ake ma sa na hada baki da wasu domin aikata damfara da kuma halarta kudin haram.
Ibori ya tsere daga Najeriya kafin a kama shi, amma an kama shi a Dubai a shekarar 2010 kuma an tafi da shi zuwa Birtaniya daga can.
Rochas Okorocha
Okorocha shi ne gwamnan jihar Imo a gabashin Najeriya tsakanin shekarun 2011 zuwa 2019, kuma EFCC ta kma shi ne ranar 13 ga watan Afrilun 2021 a ofishinsa na Unity House da ke Garki a Abuja.
Hukumar ta tuhume shi da almubazzaranci da kudaden al'umma da karkatar da wasu kudaden mallakin jihar, tuhume-tuhumen da ya musanta.
An kama Okorocha ne makwanni kadan bayan da 'yan sanda a jihar Imo suka kama shi a watan Fabrairun 2021 cewa ya sake bude wani ruunin gidajen da aka alkanta da matarsa.
Bukola Saraki
Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Olubukola Abubakar Saraki ma bai iya guje wa hukumar ta EFCC ba.
A matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, an tuhumi Saraki da aikata wasu laifuka da suka shafi kin bayana yawa da darajar kadarorin da ya mallaka.
Sai dai Kotun Kolin Najeriya ta wanke shi daga tuhumar a watan Yunin 2018.
Amma a watan Yulin 2021 hukumar EFCC ta kama Saraki kan wata sabuwar tuhumar ta satar kudaden al'umma da halarta kudin haram ta hanyar amfani da wasu abokansa da kamfanonin bogi da ke fitar da bayanan karya na shekaru masu yawa.
Orji Uzo Kanu
An daure tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor kalu na tsawon shekara 12 a kurkuku saboda an same shi da laifin aikata zamba.
Shari'ar ta samo asali ne daga lokacin da Kalu ke rike da mukamin gwamnan jihar Abia, sai dai bayan ya sauka daga mukamin az zabe shi ga mukamin dan majalisar dattawan Najeriya.
Kotu ta sami Kalu tare da wasu mutum biyu da laifin zamba kan kudin da suka kai naira biliyan 7.65 (wato dalar Amurka miliyan 19.6).
EFCC ta kuma tuhumi Kalu da wasu mutum biyu cewa sun wawushe wasu kudaden mallakin jihar ta Abia tsakanin 1999 zuwa 2007.
Peter Ayodele Fayose
A 2018 kuwa, hukumar EFCC ta saka tsohon gwamnan Ekiiti da ke kudu maso yammacin Najeriya ne a wai rukunin mutanen da ta ke bincike saboda fargabar zai tsere daga kasar bayan ya mika mulki ga sabon gwamnan jihar da aka zaba a watan Oktoban 2018.
bayan sa'a 24 a saukarsa daga mulki, Fayose ya mika kansa ga hukumar ta EFCC bayan da ya tafi can da magoya bayansa masu yawa.
Har wannan lokacin, ba a gama shari'arsa a kotu ba, kan tuhume-tuhume 11 na harta kudin haram.
Sauran tsofaffin gwamnonin da hukumar EFCC ta kama a baya:
- OSP fails to file application to challenge Charles Bissue’s writ
- Our leaders keep stealing because we lack the political will to punish them – Analyst
- Corruption is pervasive in Ghana - Ghana Integrity Initiative
- CPI report: Akufo-Addo's regime most committed in anti-corruption fight – Boakye-Danquah
- Ofori-Atta has refused to appear before PAC over corruption surrounding free SHS since 2017 – MP
- Read all related articles