Mazauna garin Saulawa cikin ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara na cikin zaman ɗar-ɗar bayan wasu 'yan fashin daji sun halaka mutum 11, sun kuma yi awon gaba da dabbobi masu yawa.
Shaidu sun ce maharan sun kuma yi alwashin sake komawa yankin na Saulawa.
Wani da ya ga abin da ya faru ya shaida wa BBC cewa yan fashin dajin sun far wa garin da karfe biyar inda suka rika harbi "ko ina kara kake ji" sannan mutanen da aka kashe sun hada da maza 10 sai mace daya.
A cewarsa yan bindigar a bakin makabarta suka yi wa mutanen da suka mutu sallah saboda sun samu rahotannin cewa maharan sun yi alkawarin komawa garin.
Ya ce makwabtan kauyuka sun kai musu ɗauki wajen jana'izar mamatan sai dai kuma an shiga firgici sanadin ikirarin da aka ce maharan sun yi.
A cewarsa "maharan sun bugo waya sun ce ko da mutanensu za su kare, sai sun kai hari a daya kauyen da ke kusa da mu".
Mutumin ya kara da cewa a lokacin da yan bindigar suka afka musu, babu wata hukumar da ta kai musu agaji.
Ita ma wata mata da harin ya yi sanadin mutuwar mijinta da babban danta da wasu yan uwanta hudu ta ce suna cikin bakin ciki matuka ganin cewa yanzu an bar ta da yara guda bakwai.
A cewarta, abincin da za su ci ma duka an kone su a yayin harin - ba komai, har gida har dukiya har babban dan" in ji ta.
A garin 'Yar Katsina cikin ƙaramar hukumar Bunguɗu kuma, mutane sama da 70 ciki har da mata masu juna biyu da ƙananan yara 'yan fashin daji suka yi awon gaba da su, baya ga ɗumbin dabbobi.
"Yan bindiga sun kwace kasuwar yar Katsina, kusan sati guda suna zagaye-zagaye sun ce ba za a yi noma ba". in ji wani da ya sha da kyar a harin.
Ya kara da cewa duk da cewa ba su kashe kowa ba a yayin harin, amma harin ya rutsa da yara kanana har da na goye da kuma manya.
Ko a jihar Neja ma, yan bindigar sun sace mutum 15 da dabbobi masu yawa a karshen mako.
Wani mazaunin Kubudi inda lamarin ya faru ya bayyana cewa maharan sun shiga yankin ne da safiya inda suka tafi da mutanen.
Hare-haren yan bindiga da yan fashin daji na ci gaba da ta'azzara a sassan Najeriya duk da ikirarin da gwamnatin kasar ke yi cewa tana kokarin ganin samun galaba a kan duk masu yi wa tsaron kasar zagon kasa.