News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Matsalar tsaro: Yan bindiga sun sace dalibai da dama a jihar Abia

 116148352 Mediaitem116148351 Matsalar garkuwa da mutane dai ta zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya

Fri, 7 May 2021 Source: BBC

Rahotanni daga jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun sace wasu ɗaliban jami'a da ba a san yawansu ba.

An yi garkuwa da daliban ranar Laraba - ranar da aka sako wasu dalibai 29 da aka sace a watan Afrilu a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin ƙasar bayan zargin an biya kuɗin fansa.

Mahukunta a birnin Umuahia sun ce ɗaliban jami'ar jihar Abia da ke Uturu na cikin wata mota ne lokacin da ƴan bindigar suka afka musu. An sace ɗaliban tare da wasu matafiya.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar John Kalu ya ce biyu daga cikin ɗaliban sun tsere daga hannun masu garkuwar yayin da sauran kuma suke hannun ƴan bindigar a wani wuri da ba a gano ba.

Matsalar garkuwa da mutane dai ta zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya.

A ranar Alhamis ne manyan hafsoshin tsaron ƙasar suka bayyana gaban majalisar dokoki domin amsa tambayoyi game da halin da tsaron ƙasar ke ciki.

Majalisar dokokin dai ta buƙaci shugaban ƙasar ya kafa dokar ta ɓaci a ƙasar wani mataki da suke ganin ka iya kawo raguwar matsalolin.

Shugaba Muhammadu Buhari na fuskantar matsin lamba kan ƙaruwar ƴan bindiga da masu iƙirarin Jihadi.

'Yan Najeriya da dama suna ganin ya gaza kare rayukansu kuma ya bar ƙasar tana ci gaba da tsunduma cikin ƙangin rashin tsaro.

Wasu ma sun yi kira a gare shi ya sauka daga mulki idan ba zai iya shawo kan matsalolin ba.

Sai dai shugaban ƙasar ya ce yana yin bakin ƙoƙarinsa.

A makon nan ne fadar shugaban ƙasar ta yi ikirarin cewa wasu malaman addini da tsoffin masu riƙe da muƙamai na siyasa suna son tayar da yamutsi da zai kai ga kifar da gwamnatin Shugaba Buhari.

Sai dai masu sharhi kan siyasa na ganin hakan wata dabara ce ta kawar da hankulan 'yan ƙasar bisa matsalolin da ke addabarsu.

Source: BBC
Related Articles: