Menu

Aƙalla mutum 20 sun mutu a rikicin ƙabilanci a Taraba

Hoton alama

Mon, 15 May 2023 Source: BBC

Akalla mutane ashirin ne suka mutu sakamakon wani rikicin kabilanci da ya barke tsakanin kabilun Wurkunawa da kuma Karimjo a Karamar Hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.

An kuma kona gidaje da dama da asarar dukiya mai dimbin yawa.

Tashin hankalin ya samo asali ne kan batun sarautar gargajiya a yankin.

A cikin makon da ya gabata ne gwamnan jihar ta Taraba Darius Ishaku ya bai wa Alhaji Yakubu Abubakar Haruna sanda a matsayin sabon sarki a masarautar Wurkum da ke Karamar Hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.

An nada sarkin ne bayan rasuwar mahaifinsa da ya shafe shekara 47 yana mulki.

BBC ta tattauna da dukkan bangarorin da ke rikici da junan kuma shugaban kungiyar ci-gaban al'ummar Wurkum na duniya Wilfred Habuba Yambakam Kwanchi, ya ce dukkan bangarori sun yi asara a rikicin.

"An dan samu zaman lafiya a cikin gari amma a kauyuka inda Wurkunawa suke har yanzu ana ta'adi, ana kona gidajen mutane sannan an kashe wasu yara.

Abincin gidaje da dabbobinsu ma duk an tafi da su, an yi asarar rayuka kuma a halin yanzu ba za mu iya cewa ga adadin mutanen ba amma sun fi goma sha biyar" a cewar Wilfred.

Ya kara da cewa gwamnati ta tura jami'an tsaro a yankin da lamarin ya auku.

Sannan yayi zargin cewa tun ranar da aka nada sabon sarki na garin wanda dan kabilar Wurkunawa ne sai 'yan kabilar Karimjo suka fara kone-konen tayoyi a cikin garin Karim Lamido.

Wilfred Habuba ya ce dama masarautar ta Wurkunawa ce sannan babu batun takara kan masarautar daga dukkan kabilu da ke yankin.

Su kuwa a nasu bangaren, 'yan kabilar Karimjo sun musanta fara tayar da hankali.

Shugaban matasa na al'ummar Karimjo Kennedy James, ya shaida wa BBC cewa ba su kai hari kan Wurkunawa ba.

"Ba mu kai hari kan Wurkunawa ba domin ba mu fada da su, a lokacin da aka nada sabon sarki sarakunanmu da kuma matasanmu sun je sun taya shi murna.

Bayan nada shi ne aka samu dan hargitsi kuma mun rasa yara kusan goma wadanda jami'an tsaro da kuma maharba suka harbe" in ji Kennedy.

A kan batun zanga-zangar da matasan kabilar Karimjo suka fara kuwa, Kennedy ya ce sun fara ta ne don nuna wa gwamnati an mayar da su saniyar ware kan masarautarsu da har yanzu ba a ba su sarki ba.

"An nada sarakuna kusan 3 a Karim Lamido amma babu kabilarmu ciki bayan mu ma muna da masarautarmu, ba a nada sarkinmu ba; Muna ganin kamar an mayar da mu saniyar-ware ne shi ya sa matasa suka yi zanga-zanga ba wai don an bai wa Wurkunawa nasu sarkin sanda ba ne" a cewar shugaban matasa na al'ummar Karimjo Kennedy James.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Taraba, kan wannan rikici, amma kokarinta bai cimma nasara ba.

Bayanai dai na nuna cewa hukumomi na ci gaba da bin matakan shawo kan matsalar, yayin da bangarorin biyu ke bayyana bukatar samar da zaman lafiya.

Source: BBC