Menu

A bai wa gwamnati lokaci kan cire tallafin man fetur - Sarkin Kano

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero

Sun, 11 Jun 2023 Source: BBC

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya buƙaci al'ummar Najeriya su bai wa sabuwar gwamnatin ƙasar lokaci game da cire tallafin man fetur domin ganin abubuwan da za ta aiwatar.

Sarkin ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan wata ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi da sarakuna daga faɗin ƙasar a fadarsa da ke Abuja.

Batun tallafin man fetur ya haifar da rashin tabbas a Najeriya, tun bayan sanarwar cire shi da Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi a ƙarshen watan Mayu.

Lamarin da ya janyo tsadar man fetur a faɗin ƙasar, tare da haifar da tashin farashin sufuri da na kayan masarufi.

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta yi barazanar shiga yajin aiki, sai dai daga baya an sulhunta tsakaninta da ɓangaren gwamnati, inda ta bayar da sanarwar janye yunƙurin nata na shiga yajin aikin, sai dai al'umma na ci gaba da kokawa kan halin da lamarin ya jefa su a ciki.

Amma a tattaunawarsa da BBC bayan kammala ganawar, Sarki Aminu ya ce gwamnati ta yi musu cikakken bayani kan lamarin tallafin na man fetur, kuma yana ganin cewa ya kamata a bai wa gwamnatin lokaci.

Ya ce "muna ganin al'umma su ƙara haƙuri, mu kuma za mu ci gaba da tattaunawa da bayar da shawarwarin yadda muke ganin al'umma za su samu sauƙin rayuwarsu bayan wannan janye tallafi da gwamnati ta yi."

Ya ƙara da cewa "Shugabannin nan ba su fi sati ɗaya ko sati biyu ba da zuwansu, ina ganin yana da muhimmanci a ba su lokaci, a aminta da abin da suka faɗa ɗin a gani.

"Idan abin da suka faɗa bai tabbata ba, daga nan al'umma za su iya kallon wannan bayani ta fuskoki daban-daban."

Shugaban Najeriya na biyar tun bayan komawar mulkin dimokradiyya a 1999, ya kawo karshen tallafin man fetur wanda aka kwashe shekaru da dama ana biya, a lokacin da ya bayyan cewa "tallafin man fetur ya kare," a jawabin rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Dan siyasar mai shekara 71 da haihuwa bai bayar da wani wa'adi kan lokaci ko tsarin da zai bi domin cire tallafin ba amma ya ce abu ne da zai gudana a hankali.

Sa'o'i kadan bayan jawabin Tinubu, daruruwan mutane suka nufi gidajen mai da motoci ko kuma dauke da jarkoki domin sayen man fetur.

Mutane kalilan ne suka yi sa'ar sayen man fetur a lokacin domin mafi yawancin gidajen sun yi ikirarin cewa man ya kare.

Tawagar shugaban ta fito ta fayyace cewa janye tallafin ba zai fara aiki ba har sai karshen watan Yuni kamar yadda kasafin kudin gwamnati mai barin gado ya tanada.

Amma wannan jawabin ya kasanec ihu bayan hari domin kuwa hankalin mutane ya riga ya tashi.

Source: BBC