Menu

Abin da ya sa na ƙi bayyana manofofina - Kwankwaso

30439509 Rabiu Musa Kwankwanso, Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party a Najeriya

Mon, 24 Oct 2022 Source: BBC

Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party a Najeriya ya ce ana ci gaba da tsare-tsare domin kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa. Kwankwaso ya ce ya kuma jinkirta bayyana manufofinsa ne domin gudun ‘satar amsa’ daga sauran jam’iyyun siyasa na ƙasar. Wasu dai na ganin Rabiu Musa Kwankwanso na jan-ƙafa wajen kafa kwamitin yayin da sauran jam’iyyu suka sanar da nasu tare da fara gangamin yaƙin neman zaɓen. A cewarsa “za mu fito ne da tsari wanda ya banbanta da na sauran ƴan takara.” Ya ƙara da cewa “Za mu fito da tsarin abin da za mu yi, da kuma yadda za mu aiwatar da shi.” Ya ƙara da cewa ya shiga dukkanin manyan jam’iyyun ƙasar biyu (APC da PDP) amma ya dawo daga rakiyar su saboda sun gaza samar da manufofin da za su ciyar da ƙasar gaba. Tarko aka kafa min a KadunaƊan takaran na jam’iyyar NNPP ya kuma yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya ƙi amsa gayyatar ƙungiyoyin Arewa domin bayyana ƙudurorinsa ga yankin. A cewar sa “...shi ya sa aka kafa tarko a Kaduna, suna so idan na je na yi bayani, daga baya su ce ga wani ɗan takara shi ya fi cancanta.” Ƴan takaran shugaban ƙasa huɗu ne suka halarci tattaunawar, wadda gamayyar ƙungiyoyi masu kare muradun arewacin Najeriya suka shirya a gidan tsohon firaiministan yankin, Ahmadu Bello. Ƙungiyoyin da suka shirya taron sun ce manufarsu ita ce su ji bayanai daga ƴan takara kan tanadin da suka yi wa yankin, sannan su faɗa wa ƴan takaran nasu buƙatun. Kuma sun musanta duk wasu zarge-zargen cewa sun shirya taron ne domin nuna goyon baya ga wani ɗan takara. Sauran ƴan takarar shugaban ƙasa sun bayyana manufofinsuA makon da ya gabata ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressive Congress, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana manufofinsa lokacin wani biki da aka gudanar a fadar shugaban Najeriya, a Abuja. A lokacin ƙaddamar da manufofin nasa, Tinubu ya ce zai mayar da hankali ne kan tsaron ƙasa, da tattalin arziƙi, da makamashi, da sauran su. A watan Satumban da ya gabata ne ɗan takaran shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar ya bayyana nasa manufofin a Abuja. A lokacin ƙaddamarwar ya yi zargin cewar Najeriya ta ɓalɓalce a ƙarƙashin mulkin jam’iyyar APC, sannan ya ce babban burinsa shi ne ceto Najeriya daga halin da take ciki, da bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma sakar wa kowane matakin gwamnati mara wajen samar da tsaro. Sai dai baya ga Rabi'u Kwankwaso, ɗaya daga cikin manyan ƴan takarar shugabancin ƙasar, wanda shi ma har yanzu bai bayyana manufofinsa ba shi ne Peter Obi. A wata tattaunawa da ya yi da BBC, Peter Obi ya ce yana jiran matsayar ƙungiyoyin ƙwadago ne kafin ya bayyana manufofin nasa.

Source: BBC