Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a ƙarshen makon nan ne, Indiya za ta wuce China a matsayin ƙasa mafi yawan al'umma a duniya.
Ana sa ran al'ummar Indiya za su kai yawan mutum biliyan ɗaya da miliyan ɗari huɗu da ashirin da biyar da dubu ɗari bakwai da saba'in da biyar da ɗari takwas da hamsin.
Lamarin kuma zai faru ne zuwa ƙarshen watan nan na Afrilu kamar yadda sabuwar ƙididdigar ta nuna.
A makon jiya ne, Hukumar kula da yawan jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA ta yi hasashen cewa yawan al'ummar Indiya zai zarce na China a tsakiyar wannan shekara.
Ƙasashen na nahiyar Asiya ne ke da fiye da kashi ɗaya cikin uku na al'ummar duniya tsawon sama da shekara 70.
"Nan ba da daɗewa ba China za ta sauka daga matsayin da ta daɗe tana kai, na ƙasa mafi yawan jama'a a duniya," kamar yadda yake cikin sanarwar da sashen kula da tattalin arziƙi da harkokin al'umma na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sanarwar ta ƙara da cewa "saboda rashin tabbas da ke tattare da ƙiyasi da hasashen yawan jama'a, ana iya nazari taƙamaimai na ranar da ake sa ran adadin Indiyawa zai zarce na China".
A makon jiya ne, UNFPA ya ce al'ummar Indiya za su kai fiye da biliyan biyu da dubu ɗari tara sama da adadin mutanen China nan da tsakiyar bana.
Alƙaluman haihuwa a China ya ragu a baya-bayan nan, inda adadin jama'ar ƙasar ya ragu bara, karon farko tun a 1961.
Akwai yiwuwar al'ummar China na iya kai wa ƙasa da biliyan ɗaya kafin ƙarshen wannan ƙarni, in ji sashen kula da tattalin arziki da harkokin al'umma na Majalisar Ɗinkin Duniya, DESA.
"Ana sa ran yawan al'ummar Indiya zai ci gaba da bunƙasa tsawon shekaru," in ji DESA.
Sai dai alƙaluman haihuwa na raguwa a Indiya daga haihuwa 5.7 ga kowacce mace ɗaya a 1950 zuwa haihuwa 2.2 ga duk mace a yanzu.
A watan Nuwamba, yawan al'ummar duniya ya kai biliyan 8.
Amma masana sun ce ƙaruwar jama'ar ba ta kai yadda take a baya ba, kuma a yanzu tana tafiyar hawainiya tun cikin 1950.