Waiwaye: Hauhawar farashi ta karu zuwa kashi 20.77 a Najeriya, ambaliyar ruwa ta kashe mutum 603 Kamar kowane mako, wannan maƙala na ɗauke da muhimman abubuwan da suka faru cikin makon da ya gabata a Najeriya. Hauhawar farashi ta karu zuwa kashi 20.77 a Najeriya Hauhawar farashi ta yi tashin gwauron zabo da kashi 20, inda ake samun karuwar tsadar kayan abinci da makamashi da kuma ci gaba da faduwar darajar kudin naira. Alkaluman hukumar kididdiga ta Najeriya sun nuna cewa hauhawar farashin ta tashi zuwa kashi 20.77 a watan Satumba daga kashi 20.52 da yake a watan Agusta, wanda ba a taba ganin irin sa ba tun shekarar 2005. Kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo zuwa kashi 23.4, idan aka kwatanta da kashi 23.1 da yake a watan Agusta. Ana kuma ganin cewa matsin lamba zai iya sanya kwamitin tsare-tsare mai kula da kudi na Babban Bankin Najeriya ya kara yawan bashi da yake ciyowa a karo na hudu a jere a watan Nuwamba. Buhari ya karrama Jonathan da Wike da lambobin yabo kan kwarewar aiki Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da kuma tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan lambobin yabo kan kwarewar aiki a wani biki da aka yi a fadar shugaban Kasar da ke Abuja yau. Ga baki daya fitattun ‘yan kasar 44 aka karrama da lambar yabon wadda aka kira da Nigeria Excellence Award in Public Service (NEAPS). Wadanda aka karraman sun hada da gwamnonin jihohin kasar 16 da Shugaban Majalisar Dattawan kasar Ahmad Lawan, da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da kuma manyan hafsoshin rundunonin soji na kasar. A jawabinsa Sakataren gwamnatin tarayyar kasar Boss Mustafa wanda ofishinsa ne ya jagoranci shirya bayar da wannan kyautar da hadin wata cibiya mai zaman kanta da ake kita TBS, ya ce an fito da bayar da kyautar ne domin karrama wadanda suka nuna gogewa wajen yi wa kasar hidima a dukkan matakai. Gwamna Umaru Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa na daga cikin gwamnonin aka ba kyautar ta NEAPS wadda ita ce irin ta farko a kasar. Wadanda suka shirya bayar da wannan yabon dai sun ce kafin mutum ya cancanci samun wannan lambar yabon dole ne ya kasance jami'in gwamnati ko mutum mai zaman kansa da da ke raye wanda ya nuna bajinta a fannin da yafi kwarewa kuma ya kasance mai halaye na-gari. Ma’aikatar jin kai ta Najeriya ta fitar da sabbin alkaluman na yawan adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar. Ministar ma’aikatar Sadiya Farouk, ta ce yawan mutanen sun kai 603. Sannan kuma an kiyasta cewa mutane fiye da miliyan daya da dubu 300 ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliya ruwa a fadin kasar. Ministar ta ce: ”Akwai wadanda suka ji raunuka sakamakon ambaliyar wanda yawansu ya kai 2,407,, sannan kuma akwai gidaje dubu 121, 318 da ambaliyar ta shafa.” Sadiya Farouk, ta ce akwai kuma gidaje fiye da 82,000 da suka rushe gaba ɗaya. Ministar ta ƙara da cewa sakamakon abin da ya faru a bana, akwai matakan da ya kamata a dauka na kauce wa samun irin wannan mummunar asara, kamar kwashe mutanen da ke zaune a yankunan da ke gabar ruwa. Ba mu dakatar da samar wa 'yan Najeriya iskar gas ba - NLNG Kamfanin samar da iskar gas na girki a Najeriya, Nigeria LNG Limited (NLNG), ya musanta rahotannin da ke cewa ya dakatar da aiki a wasu masana'antunsa da ke kudancin ƙasar saboda ambaliyar ruwa. Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter, NLNG ya ce dukkan masana'antunsa na aiki "duk da cewa ba yadda suka saba ba saboda ƙarancin gas da yake fuskanta daga abokan hulɗarsa". Tuni aka shiga fargabar hauhawar farashin gas ɗin saboda tsoron ƙarancinsa a kasuwa bayan kamfanin ya ba da sanarwar rage yawan gas ɗin da yake samarwa saboda raguwar da aka samu daga abokan hulɗarsa da ke samar masa da ɗanyen gas, wanda ambaliyar ta haifar. "Babu wata masana'antarmu a Tsibirin Bonny ko kuma wani wuri da ta fuskanci matsala sakamakon ambaliyar ruwa," a cewar kamfanin. NLNG ya ce yana ci gaba da samar wa kasuwar cikin gida gas ɗin daga abin da yake da shi a rumbunsa kuma yana ci gaba da lalubo hanyoyin magance matsalar da ambaliyar ta haifar wa abokan hulɗar tasa. APC da PDP a Zamfara na zargin juna da kai hari kan magoya bayansu Ana ci gaba da cacar baki tsakanin ƙusoshin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, da na jam'iyyar hamayya ta PDP, kan wasu zarge-zargen hare-hare da bangarorin biyu ke yi wa juna. Jam'iyyar APC dai na zargin wasu 'yan jam'iyyar PDP da kai wa magoya bayanta hari, inda suka kashe mutum guda da kuma raunata wasu fiye da 10. APC ta ce an kai wa magoya bayan nata da ke share-share hari ne a Gusau babban birnin jihar. Malam Yusuf Idris Gusau, shi ne sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC a jihar, kuma ya shaida wa BBC cewa “matasan waɗanda magoya bayan jam’iyyarmu ne na aiki a GRA, sai kawai ga magoya bayan jam’iyyar PDP kuma nan take suka fara kai musu hari da bindiga.” Ya ci gaba da cewa: “Batun ace magoya bayan namu ne suka takali fada sam ba haka bane, domin da hakan ne da suma an gansu da bindiga har ma su yi harbi.” Rikicin Boko Haram ya sanadin rayuka 100,000 tare da asarar naira tiriliyan 3.24 Babban Hafsan Tsaro na Najeriya Janar Lucky Irabor ya ce rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutum 100,000, yayin da ya raba mutum miliyan biyu da muhallansu. Kazalika, yaƙin ya janyo hasarar kusan naira tiriliyan 3.24. Jaridar Daily TrustJanar Irabor ya fadi haka a ranar Talata a lokacin rufe bikin bitar ayyukan ministocin kasar da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar. Ya kuma tabbatar da cewa hukumomin sojin kasar sun karbi naira tiriliyan 2.5 a kasasfin kudi cikin shekara bakwai da suka gabata, amma duk da haka kashi 35 cikin 100 ne kacal na abin da suke nema. 'Yan Boko Haram na kafa sansanoni a garuruwan Zamfara' Gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta samu rahotonnin da ke cewa kungiyar Boko Harama tsagin ISWAP na kokarin kafa sansanoni a kauyen Mutu na gundumar Mada da ke Gusau babban birnin jihar. Shugaban kwamitin shigar da kara da laifukan da suka shafi fashin daji kuma mamba a kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri na jihar, Dakta Sani Abdullahi ya ce 'yan ISWAP sun shiga jihar ne ta yankunan Danjibga da Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe. Ya kara da cewa a baya-bayan nan, mayakan kungiyar suna yawaita kai hare-hare kan garuruwa da kauyuka masu yawa a fadin jihar. Mutum 14 sun rasu a haɗarin kwale-kwale a Sokoto Hukumomi a Sokoto sun tabbatar da mutuwar mutum 15 a wani haɗarin wani jirgin ruwa da ya faru a ƙaramar hukumar Shagari. Lamarin ya faru ne ranar Talata a kusa da wani ƙauye da ake kira Sulluɓawa. Shugaban ƙaramar hukumar Shagari Alhaji Aliyu Dantani ya tabbatar wa BBC cewar kwale-kwalen na ɗauke ne da mutum 24, inda 10 daga cikin su suka tsira, yayin da guda 14 suka rasa rayukansu. Akasarin waɗanda suka rasa rayukan nasu dai maza ne, inda mata uku ne suka mace a cikin 14. Bayanai sun ce matafiyan suna kan hanyarsu ne ta komawa gida bayan halartar bikin Maulidi. Mutanen da suka rasu a cewar shugaban ƙaramar hukumar sun fito ne daga ƙauyuka daban-daban kamar ƙauyen da ake kira Gidan dawa, da Sabon garin sulluɓawa, da kuma Tsohon garin sulluɓawa.