Harry Kane shine kan gaba a ci wa tawagar Ingila a cin kwallaye a tarihi, wanda ya fara cin kwallo a rana irin wannan a 2015.
Kane ya shiga karawar a minti na 80, bayan da ya canji dan wasa a fafawar da Ingila ta casa Lithuania 4-0 a Wembley.
Lokacin da Kane ya shiga wasan ya sha tafi daga magoya baya, kuma taba kwallon farko ya zura a raga ta wuce golan Lithuania.
Wadanda suka ci wa Ingila kwallayen tun farko sun hada da Wayne Rooney da Danny Welbeck da kuma Raheem Sterling .
To amma a lokacin jaraidu su ka yi ta labarin kwazon Kane, lokacin da Ingila ke buga wasannin neman shiga Euro 2016.
Ranar Almahis Kane ya kafa tarihin yawan cin kwallaye a tawagar Ingila, bayan da suka doke Italiya 2-1.
Kane ne ya ci na biyu a bugun tazara a Italiya a wasan farko a rukuni a neman shiga Euro 2024.
A ranar Alhamis ya ci na 54 ya haura Wayne Rooney mai 53 a tarihin ci wa tawagar kwallaye a baya a tarihi.
To sai dai dan wasan Tottenham ya kara ci wa Ingila a 2-0 da suka doke Ukraine ranar Lahadi a Wembley a wasa na biyu a rukuni, domin shiga gasar nahiyar Turai.
Kenan Kane ya ci kwallo 55 a wasa 82 da ya yi wa tawagar Ingila tun daga 2015 kawo yanzu a tarihi.
Cikin kwallayen da Kane ya ci har da shida da ya zura a raga a gasar kofin duniya a Rasha a 2018, wanda ya zama na uku dan kasar da ya lashe takalmin zinare a babbar gasar tamaula a duniya.
Na farko mai bajintar shine Garry Lineker a gasar kofin duniya a 1986 da kuma Alan Shearer a gasar nahiyar Turai a 1996
Ya kuma kafa tarihi da yawa a tawagar Ingila, shekarar da yafi cin kwallaye ita ce ya zura 16 a raga a farkon shekarar 2021 zuwa karshenta.
Kane yana da jan aiki a gabansa idan yana fatan kalubalantar Cristiano Ronaldo mai kwallo 122 a yawan zura wa tawaga a tarihi.
Kwallo 204 da ya zura a raga a Tottenham ya zama na uku a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League.
Ga jerin 'yan wasan Ingila da suka ci mata kwallo sama da 40: