BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

APC ta tabbatar da goyon baya ga Sen Akpabio don shugabancin majalisa ta 10

Godfather Akpabio.png Sanata Godswill Akpabio

Mon, 8 May 2023 Source: BBC

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta amince da rabon mukamai na shugabancin majalisa ta goma.

Ta ce ta amince da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattijai daga shiyyar Kudu maso Kudu.

Haka zalika, Sanata Barau Jibrin zai kasance mataimakin shugaban majalisar dattijai daga Arewa maso Yamma.

Wata sanarwa da jam'iyyar mai mulki ta fitar, ta ambato kwamitin gudanarwa na APC yana cewa matakin ya zo ne bayan rahotannin tuntuba da tarukan da jam'iyyar ta yi da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu

Muna tafe da karin bayani......

Source: BBC