Menu

Abin da Firai Ministan Burtaniya ya shaida wa Zalensky kan neman jiragen yaƙi

60896466 Rishi Sunak da Volodomyr Zalensky

Thu, 9 Feb 2023 Source: BBC

Da alama bukatar Shugaban Ukraine Volodomyr Zalensky ta kasashen Turai da su taimaka wa kasarsa da jiragen yaki domin fuskantar kasar Russia a yakin da suke yi, ba ta samu shiga ba a wannan karo.

Zalensky wanda ya mika wannan bukata a taron shugabannin kasashen Turai a Brussels ranar Alhamis, ya ce “ban ga alamar karewar wannan yaki a kusa-kusa ba saboda haka muna neman tallafinku domin kare rayuwar nahiyar Turai baki dayanta.”

Ya kara da cewa “barazanar da Russia ke yi ba wai kawai ga Ukraine ba ne, abin na barazana ga rayuwar Turawa ne baki daya. Saboda haka ya zama wajibi mu tunkare ta.”

To sai dai da alama Mista Zalensky bai samu abin da yake so ba domin Burtaniya ta ce ba yanzu ba.

Firai ministan Burtaniya, Rishi Sunak ya shaida wa Volodomyr Zalensky cewa matakin farko da za su dauka na tallafa wa Ukraine da jiragen yaki shi ne bai wa mataukan jiragen yaki na kasar horo na musamman.

Ya kuma kara da cewa “Burtaniya ce kasa ta farko wadda za ta fara bai wa sojojin saman kasar Ukraine horo ta hanyar amfani da jiragen yaki da dokar NATO ta tanada.

Da me Ukraine ke yakar Russia?

Fiye da kasashe 30 ne dai suka bai wa Ukraine gudunmuwar kayan yaki tun kutsen da Russia ta yi mata a bara.

Kayan yakin da kasashen suka aike da su Ukraine sun hada da tankokin yaki da motoci da roket masu dogon zango da sauran makaman da ke dakile hare-haren sararin samaniyya.

Kafin zuwansa Brussels din, shugaba Zalensky ya je Burtaniya inda ya gana da ‘yan majalisar dokoki da wasu jiga-jigan siyasar kasar duk a wani mataki na neman karin gudunmowar Turawa bisa yakin da yake yi da Vladimir Putin na Russia.

A ranar Alhamis ne kuma Kamfanin tauraron dan adam na SpaceX ya takaice irin abin da kasar Ukraine za ta iya yi da tsarinsa na intanet ta fuskar yaki.

Rahotanni ne dai ke nuna cewa Ukraine din ta yi amfani da tsarin intanet na kamfanin wajen sarrafa jirage marasa matuka.

Kamfanin dai ya bai wa Ukraine din damar yin da dubban kwanukan tauraron dan adam wanda ke bai wa jama’a damar kallo da kuma samun tsarin intanet.

To sai dai an ce Ukraine din na zarmewa wajen yin amfani da tsarin intanet na kamfanin domin kai wa Russia hare-hare – wani abu da ke nuna ta karya ka’idar kamfanin na SpaceX.

Source: BBC