Menu

Abin da ke zahiri ya tankwaɓe fatan zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasɗinawa

Hoton alama

Wed, 19 Apr 2023 Source: BBC

Tashin hankalin da ke faruwa tsakanin Isra’ila da Palasdinawa na kara ta’azzara, inda fatan da ake da shi na samun zaman lafiya da warware matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu ke da kamar wuyar faruwa.

Kudus birni ne mai tsarki ga wadanda suka yi imani da hakan.

Yanayin wurin a nan kan kasance cike da karar hayaniya mai karfi a lokacin da mabiya ke bikin hutun addini, musamman ma a tsohon birnin mai zagaye da bango inda wurare masu tsarki na Kiristoci da Yahudawa da Musulmai suka kasance ga baki-ga-hanci da juna.

Addini na da wani muhimmanci da kuma karfi a nan da yake da matukar wahala a iya kururutawa.

Hakan kuwa saboda ya shafi addini fiye da daya kawai. A birnin Kudus ana danganta shi da Palasdinu da Isra’ila. Addini, da siyasa da asali na yin tasiri ga juna.

Bangarorin biyu masu gogayya da juna na girmama tsarkakar birnin na Kudus tare da ikirarin cewa babban birnin su ne.

Wannan watan na Ramadan, da bukukuwan Passover na Yahudawa da na Easter na Kiristoci sun zo a lokaci guda. Sun kuma zo a daidai lokacin karuwar yanke kauna da kuma fargaba da hadari.

Shekaru biyu da suka gabata, tsaurara dokokin Isra’ila a kan Palasdinawa lokacin watan Ramadan daya daga cikin abubuwan da suka rura wutar tashin hankali mai muni ne a yankin Gaza tsakanin Yahudawa da kungiyar Hamas ta Palasdinawa.

Ya nuna alamun kamar akwai yiwuwar hakan zai sake faruwa a cikin wannan watan, lokacin da jami’an tsaron Isra’ila suka kutsa cikin Masallacin al- Aqsa, inda Musulmai suka yi amanna nan ne Annabi Mohammadu (SAW) ya hau zuwa aljanna.

‘Yan sanda sun yi amfani da dabaru na mugunta wajen fitar da Palasdinawa da suka kulle kansu a cikin masallacin.

Hoton bidiyon ‘yan sanda dauke da manyan makamai na lakada wa Palasdinawa duka ya haddasa fusata a fadin yankin Gabas ta Tsakiya da sauransu, da suka hada da kasashen Larabawan da suka sasanta dangantakarsu da Isra’ila.

Harin rokoki da suka fada kan Isra’ila da kasar Lebanon, mai yiwuwa daga kungiyoyin Palasdinawa, inda suka haddasa shiga mummunan hali mai cike da hadari a kan iyakar da aka girke makamai masu tarin yawa tun bayan da kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta far wa Isra’ila a shekarar 2006.

A cikin kwanakin tun bayan wannan samame a al-Aqsa, duka bangarorin sun janye daga sake yin wani fito-na-fiton abubuwan fashewa, amma dalilan da suka sa suka kai ga wannan mataki har yanzu na nan.

Ya kai fiye da shekaru 10 tun bayan wani yunkurin da aka yi na saka Palasdinawa da Yahudawa su tattauna a kan makoma, ta zama tare ko kuma rabuwa.

Lokutan da aka shafe na zaman rashin tabbas ya ja hankulan shugabannin Isra’ila musamman firaminista mafi dadewa a kan mulki, Benjamin Netanyahu, cewa za a iya sassauta tashin hankalin amma ba sasantawa ba.

Shekaru biyu na karuwar rashin jituwa da tashin hankalin tun bayan yakin Gaza sun yi nuni da yadda hakan ya zama akwai shakku a ciki.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Turai da sauran su har yanzu na nanata amannarsu cewa dama daya kadai ta samun zaman lafiya ita ce samun bakin zaren warware matsalolin bangarorin biyu – samar da kasar Palasdinu mai cin gashin kan ta.

Wannan tsari ne na cewa kasar Palasdinu mai cin gashin kanta tare da Isra’ila zai bayar da dama ga duka bangarorin biyu su zauna lafiya da junansu.

Na tuka mota daga birnin Kudus daga Hebron don tunatar da kaina game da wasu dalilan da suka saka.

Shiga cikin motar tare da tukawa cikin wannan hanya, kamar yadda na sha yi tun a shekarar 1990, ya sake nuna irin banbancin da ke tsakanin irin burin kasashen waje game da makomar wannan yanki da ainihin halin da mutanen da ke rayuwa a nan ke ciki.

Na tuka mota a daidai lokacin da ake wata gagarumar guguwa a gabar Yammacin Kogin Jordan ga kuma saukar ruwan sama mai tafe da iska.

Zan iya ganin shaida iri daya cikin sauki da a ce na shiga ta arewaci ko gabashin birnin Kudus a maimakon kudanci.

A cikin shekaru tun bulaguron farko da na yi tsakanin Kudus da Hebron, yanayin tafiyar da kuma gefen hanyoyin sun sauya.

A farkon shekarar 1990 hanya ce ta karkara. Matsugunan Yahudawa kadan ne ake iya gani jefi-jefi daga kasan tsaunuka, musamman kusda da birnin Bethlehem, garin Palasdinu na farko hanyar na wucewa a yayin da kake barin birnin Kudus.

Amma galibin wuraren da ke bakin hanya sarari ne fetal da Palasdinawa manoma suka nome. Wasu daga cikinsu kan tafi zuwa aikin ta hanyar amfani da jakuna.

Har yanzu manoman na noma amfanin gona, amma gonakin sun ragu saboda gagarumin aikin fadada matsugunai.

An kwace tarin filayen Palasdinawa da dama don kara fadin hanya, da kuma hada hanyoyin da ke hada matsugunan da sauran da kuma birnin Kudus.

Sabbin hanyoyin sun samu ne ta hanyar banbaro wasu tsaunuka.

A cikin wannan makon hanyar birinin Kudus zuwa Hebron ta cika da ababan hawa.

Motoci da dama na dauke da lambobin Isra’ila, da ke nuni da gagarumar karuwa a yawan al’ummar Yahudawa a yankin matsugunan.

Yayin saukar ruwan sama, akwai gomman sojojin Isra’ila dauke damarar yaki suna kai komo a kusa da manyan motocinsu a wasu sabbin ayyukan soji a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye har na tsawon shekaru 56, ba tare da nuna wata alamar kawo karshe ba.

Suna kusa da wata hasumiyar hange ta sojoji da ke kusa da mashigar Beit Ummar, wani karamin garin Palasdinawa da mazaunansa akasari suka dogara ga ayyukan noma don tafiyar da rayuwarsu.

Beit Ummar, kamar sauran garuruwa da kauyuka a yankin Gabar Yammancin Kogin Jordan, na da manyan filaye na hanyoyi.

Kama-wuri-zaunan, da burin jajircewa a kai, ya haifar da yawan tashe-tashen hankula a cikin tsawon shekaru.

Akasarin kasashen duniya na daukar matsugunan Isra’ila a yankunan a matsayin ba bisa ka’ida ba.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na Amnesty International da Human Rights Watch na cikin jerin kungiyoyi masu fafutika da ke cewa ayyukan Isra’ila a yankunan kama-wuri-zauna sun haifar da nuna wariyar launin fata.

Isra’ila ta musanta zargin tana mai cewa dokokin kasa da kasa da ke hana wata kasa ta tsugunar da mutanenta a yankin da ta mamaye basu shafi wadannan yankuna ba.

Biliyoyin dalolin da Isra’ila ta kashe a cikin shekaru da dama wajen gina hanyoyi, da gidaje, da duk wani tsaro da ake bukata a kare Yahudawa mazauna wurin, sun haddasa sabbin batutuwa, da ke nufin tabbatar da cewa Isra’ila za ta iya rike ikon yankuna da dama da ta kwace a lokacin yakin yankin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967.

Gwamnatin Isra’ila ta fadada matsugunan, a daidai lokacin da suke magana game da batun warware matsalolin bangarorin biyu.

Sabbin dokokin gwamnatin hadaka sun fi zama kai tsaye. Sun yi nuni da cewa gwamnati, wadda har ila yau ke karkashin Benjamin Netanyahu, ita ce mafi kishin kasa a tarihin kasar Isra’ila.

Gwamnati ta bayyana cewa za ta assasa tare da bunkasa matsuguna a kan filayen da Yahudawa ke da cikakken ‘yanci’’.

Fadada matsugunan ba shi ne kadai dalilin da ya sa zaman sasantawa tsakanin Palasdinawa da Yahudawa ya gagara ba.

Amurka, wadda ta dauki nauyin zaman tattaunawar a baya, na da wata damuwar. Ta fi damuwa da gogayyarta da kasar China da kuma yakin da ke faruwa a Ukraine.

Shugabancin siyasar Palasdinu ya samu rarrabuwar kai matuka tsakanin kungiyar Hamas a Gaza da hukumar Palasdinawa a gabar Yammacin Kogin Jordan.

Ba za su iya yin komai ba, idan aka duba yadda abubuwa suke, na yin wani katabus na yarjejeniya.

Da matukar wahala Hukumar Palasdinawa ta iya yin wani katabus na amfani da wani karfin da take da shi.

Isra’ila na cikin nata matsalolin cikin gida na siyasa game da dimokradiyyarta.

Wanzuwar zaman lafiya tsakanin Palasdinawa da Yahudawa na da kamar wuya. Babu ko wane bangare da ya yarda da juna.

A cikin wannan shekarar wani mummunan tashin hankali da mace-mace babban gargadi ne na karuwar mafi munin tashin hankali nan gaba.

Kowa a nan ya san da hadarin da suke shiga. Babu wanda yake da wani ingantaccen tsari na shawo kan mummunan tashin hankalin da ke shirin kunnowa nan gaba.

Source: BBC