BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Abin da muka sani game da jirgin ruwan da ya ɓata a ƙarƙashin teku

Polar Prince, jirgin ƙarƙashin tekun

Wed, 21 Jun 2023 Source: BBC

Ana ci gaba da wani gagarumin aikin bincike da ƙoƙarin ceto a tekun Arewacin Atalantika bayan wani jirgi ko sunduƙi mai tafiya a ƙarƙashin teku, don ganin tarkacen jirgin Titanic ya ɓace a can ƙarƙashin teku ranar Lahadi.

Mutum biyar ne a cikin jirgin ƙarƙashin tekun.

Masu bincike a cikin jirgin ruwan Polar Prince - babban jirgin da ke ɗauke da sunduƙin zuwa ƙarƙashin teku daga saman ruwa - ya rasa sadarwa da ma'aikatan jirgin jim kaɗan bayan ya fara nutso a cikin teku.

Iskar numfashi ta oksijin da ke cikin jirgin taƙaitacciya ce kuma ana ƙiyasin cewa kayan masarufin da ke cikin jirgin za su iya ƙarewa da misalin ƙarfe 10:00 agogon GMT a ranar Alhamis.

An jiyo wasu ƙararraki yanzu a yankin da ake bincike, amma dai ba a san daga inda ƙarar take fitowa ba da kuma abin da suke nufi.

Hukumomin Amurka da Kanada da kuma na Faransa na aiki tare don gano inda jirgin ko sunduƙin ƙarƙashin teku yake, kuma kamfanin shirya yawon shaƙatawa na OcenGate ya ce yana bin diddigin duk zaɓin da ake da shi don ganin an tsamo jirgin cikin aminci.

Ga abubuwan da muka sani zuwa yanzu.

Mene ne sabon labari game da aikin bincike?

Wani jirgin saman ƙasar Kanada mai aikin bincike ya jiyo hayaniya a can ƙarƙashin teku.

Ƙwararru kan al'amuran ƙarƙashin teku sun ce da wuya a iya tantance ko wannan hayaniya, ta mene ne matuƙar ba a nazarci bayanai ba.

Sai dai hayaniyar da ake ji mai yiwuwa ne ƙara ce taƙaitacciya kuma mai kaifi daga cikin jirgin lokacin da ya ci karo da wani abu mai tauri a ƙasan teku.

Jami'an tsaron gaɓar tekun Amurka sun aika wasu jiragen ƙarƙashin teku da ake sarrafa su daga nesa, don gudanar da bincike a farfajiyar wurin.

Akwai jiragen sama da ke ci gaba da lalube daga sararin sama, ko da jirgin Titan da ke tafiya ƙarƙashin teku ya dawo saman ruwa amma kuma ya gaza sadarwa.

Ana sa rai da yammacin nan ne kuma wani jirgin ruwan Faransa mai ɗauke da butum-butumi mai shiga ƙasan teku zai isa wurin binciken.

Source: BBC