BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Abin da ya sa Mali ke son korar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Ɗinkin Duniya

Fri, 30 Jun 2023 Source: BBC

Gwamnatin Mali ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwashe dakarunta na wanzar da zaman lafiya 13,000 daga ƙasar bayan kwashe shekaru 10 suna aiki a ƙasar.

A bara ne Faransa ta janye nata dakarun, bayan da sojoji suka ƙwace mulkin ƙasar , tare da gayyato mayaƙan Wagner daga Rasha.

Me ya sa MDD ta tura dakarunta zuwa Mali?

A shekarar 2013 Majalisar Dinkin Duniya ta ƙaddamar da shirinta na wanzar da zaman lafiya a Mali bayan da ƴan aware da kuma masu da'awar jihadin Islama sun haɗe wuri guda tare da mamaye yankin arewacin Mali.

Sun yi hakan ne da sunan kafa wata sabuwar ƙasar ta daban.

Dakarun wanzar da zaman lafiyar na MDD sun isa ne bayan Faransa ta tura dakarunta 5,000 domin yayyafa wa rikicin ruwa.

Sai dai matsalar tsaron ta masu da'awar jihadi waɗanda suka yi sanadin rayukan dubban mutane ta ci gaba da zama barazana na tsawon shekaru.

Yayin da aikin dakarun na wanzar da zaman lafiya ya ƙunshi kare fararen hula daga hare-haren ƴan bindigar, ba su je ƙasar da niyyar kai hare-hare a kan mayaƙan ba.

A Mali, da yankin Sahel, ƙungiyoyin IS da, al-Qaeda da ke kiran kanta Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin sun riƙa kai hare-hare.

Sai wata ƙungiyar da ke kiran kanta Ansaroul Islam da ke kai hare-hare a Burkina Faso, da kuma Boko Haram wadda ke kai nata hare-haren a ƙasashen da ke gefen tafkin Chadi.

Shin dakarun MDD sun yi nasara?

Duk da cewar akwai dakarun Majalisar Dinkin Duniya da na Faransa a Mali domin aikin wanzar da zaman lafiya, hare-haren masu iƙirarin jihadi sun ƙaru, haka nan ma yawan matasa da ke shiga ƙungiyoyin sun ƙaru.

A tsawon shekaru goma da suka gabata an kashe sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD akalla 300 a Mali.

Wannan ne asarar dakaru mafi yawa da ta yi a wani shiri na wanzar da zaman lafiya a faɗin duniya.

Rasha da China sun soki shirin na MDD a Mali, kuma ƙasashe kamar Birtaniya da Sweden sun daina tura sojojin nasu a ƙarƙashin shirin.

A bara ne shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce zai janye dakarun Faransa daga ƙasar.

Ya fusata ne kasancewar sojojin da suka ƙwace mulki a 2021 sun jinkirta shirin miƙa mulki ga farar hula.

Sannan gwamnatin sojin ta gayyato mayaƙan Wagner domin samar da tsaro, wadda za ta samar da mayaƙa kimanin 1,000.

A wancan lokaci babu masaniyar cewa ko boren da Wagner ta yi a Rasha zai yi wani tasiri a ayyukanta a Mali.

Me ya sa Mali ke son dakarun wanzar da zaman lafiya su fice daga ƙasar?

Aikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali zai ƙare ne a ranar 30 ga watan Yuni.

Sai dai Sakatare-Janar na MDD, Antonio Guterres ya bayar da shawarar tsawaita zaman dakarun a Mali da shekara ɗaya.

To amma Ministan harkokin waje na Mali, Abdoulaye Diop ya ƙi amincewa da hakan, inda ya ce dakarun MDD ba su taka rawar da ta dace ba wajen magance matsalar tsaron ƙasar.

Kwamandojin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD sun sha kokawa kan cewa gwamnatin Mali na yin katsalandan a cikin ayyukansu.

A nasa ɓangaren, Mista Diop ya zargi dakarun wanzar da zaman lafiyar da yin zarge-zarge masu nauyi a kan gwamnati waɗanda suka yi cikas ga batun sasantawa da samar da zaman lafiya a ƙasar."

A watan Mayu, wani rahoto da MDD ta fitar ya yi zargin cewa dakarun da gwamnatin Mali ta yi hayarsu sun kashe fararen hula 500 a wani yunƙurin kai farmaki kan masu iƙirarin jihadi a tsakiyar ƙasar Mali, a watan Maris na 2022.

A ranar 30 ga watan Yuni ne Kwamitin tsaro na MDD zai kaɗa ƙuri'a kan yadda za a janye dakarun wanzar da zaman lafiyar daga Mali.

An fahimci cewar MDD za ta tattauna ne kan shawarar Faransa na janye dakarun a hankali a cikin wata shidda.

Source: BBC