Menu

Abin da ya sa Wigan ta sallami Kolo Toure

Kolo Toure

Fri, 27 Jan 2023 Source: BBC

Wigan Athletic ta sallami kocinta Kolo Toure bayan ya buga wasa tara ba tare da kungiyarsa ta samu nasara ba.

A watan Nuwamba ne aka nada tsohon dan wasan Arsenal da Manchester City a matsayin kocin da ya maye gurbin Leam Richardson.

Sai dai maki biyu kacal kungiyar Wigan ta samu a cikin wasa bakwai a gasar Championship.

"Matakin mai wuya ne amma hakan ne kaiwa zai bamu damar ci gaba da kasancewa a gasar Championship a kakar wasa mai zuwa," in ji shugaban Wigan Malachy Brannigan.

"Ina godiya ga Kolo saboda aikin da yayi tare da mu."

Toure a kasance mataimakin Brendan Rodgers a Celtic da kuma Leicester kafin Wigan da dauke shi a cikin watan Nuwamba.

Source: BBC