Menu

Abincin Italiyawa da ake sarrafawa da ƙwari

Hoton alama

Mon, 17 Jul 2023 Source: BBC

A cikin wani karamin daki da ke kusa da tsaunukan arewacin Italiya, wasu manyan mazubai ne makare da miliyoyin fara a cikinsu.

Yayin da suke tsalle da kuka, wadannan miliyoyin kwari na dab da zama abinci.

Akwai hanyoyi da ake bi wajen gyara tare da tanadinsu.

Akan gasa su, ko a dafa su, ko a soya su, ko kuma nika su domin sarrafawa ta hanyoyi daban-daban.

Nan a gonar fari da ke Italiya, gonar kwari mafi girma a kasar, kusan fari miliyan daya ake amfani da su wajen hada sinadarin abinci a kowacce rana.

Ivan Albano, wanda ke kula da gonar, ya bude wani katon mazubi domin nuna mana wai sinarin da ake amfani da shi wajen yin taliya da burodi da gurasa da lemo da sauransu.

Cin fara, da tururuwa da gwazarma ba wani sabon abu ba ne a wasu sassan duniya kamar yankin Asiya da aka kwashe dubban shekaru ana cin fari.

A yanzu bayan da Tarayyar Turai ta amince da sayar da kwari a matsayin abincin dan adam a wannan shekara, shin za a samu sauyi a wasu kasashen Turai?

A yanzu a duka fadin Turai babu wata kasa da mutanenta ke kyamar cin kwari irin Italiya, kamar yadda bayanan kamfanin YouGov mai lura da ra'ayoyin mutane, ya bayyana.

Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na haramta amfani da kwarin wajen yin pizza da taliya a kasar.

"Ba za mu yadda da wannan dabi'a mara kyau ba, a cikin kasarmu, domin kuwa hakan zai lalata mana tsarin noma da al'adunmu,'' kamar yadda mataimakin firaministan kasar Matteo Salvini ya rubuta a shafinsa na Facebook.

To za a samu sauyi kuwa? masu kamfanoni da dama a Italiya sun kware wajen amfani da sinadarin fari don yin taliya da pizza da sinasir.

To amma mai lura da gonar farin ya ce ''abin da muke yi yana da matukar kyau, saboda muna amfani da ruwa lita 12 ne kawai wajen samar da kilo daya na garin sinadrin fari''.

Yana mai cewa idan za a samar da sinadarin ta hanyar amfani da naman shanu to dole ana bukatar dubban litar ruwa.

Kiwon fari na bukatar 'yar karamar gona wadda ba mai girma ba, idan aka kwatanta da gonakin samar da nama.

Masu bincike da dama sun yi imanin cewa kiwon fari wata hanya ce da za ta iya magance matsalar sauyin yanayi.

A wani gidan cin abinci da ke birnin Turin, mai dafa abincin mai suna Simon Loddo na amfani da sabuwar taliyar da aka kwashe shekara kusan 1000 ana amfani da ita a kasar, wadda a yanzu kashi 15 cikin 100 na sinadaranta daga fari ake samunsu.

Wasu daga cikin masu cin abinci, sun ce ba sa bukatar abincin da aka yi da sinadarin fara, to amma wadanda suke so, ciki har da ni mun ji mamakin yadda take da dandano mai dadi.

Baya ga dandano mai dadi, abinci ne mai dadi da ke kunshe da sinadaran Vitamins da Fibre da sinadarin amino.

To amma wannan zai zama mafita ga mutanen da ba sa son cin nama? Babbar maganar ita ce farashi.

‘’Abincin da ke dauke da sinadarin fari ya fi tsada fiye wanda ba shi da shi, ana kashe kudi masu yawa wajen yin sinadarin, kusan dala 42 kan kowanne kilogiram, don haka taliya gida daya da aka yi da sinadarin fari yakan kai yuro 8.’'

A yanzu abinci da aka yi da kwari ya kasance abincin da kasashen yamma ke marari, yayin da a yanzu farashin kaji da nama ke ci gaba da raguwa.

‘’Naman da ake samarwa yana da araha idan aka kwatanta da garin sinadirin fari, duk kuwa da yawansa’’, in ji Claudio Lauteri, wanda ke da gona a kusa da birnin Rome.

To amma ba maganar farashi ce kadai ba, magana ce kan yadda al’umma suka karbe shi.

A duk fadin Italiya ana samun karuwar mutanen da suka kai shekara 100 ko fiye.

Kuma da yawa na danganta hakan da irin nagarta da ingancin abincin da suke ci.

‘’Mutanen Italiya sun shafe ysawon karni mai yawa suna cin nama wanda ke kara musu lafiya’’, in ji Claudio

Ya ce ya yi amanna cewa sabbin abincin da ke dauke da garin sinadarin fari na iya yin barazana ga karuwar tsoffi masu lafiya da kasar ta yi fice da shi tsakanin takwarorinta.

‘’Bana goyon bayan wadannan sabbin nau’ikan abinci. Don haka ba ma na cin su’’.

A yayin da noman kwari ke habaka a Turai, ana ci gaba da samun masu adawa da shirin.

Wani mamba a jam’iyya mai mulki a Italiya ya bayyana matakin halasta amfani da kwari a matsayin abinci dan adam da Tarayyar Turai da amince da shi da cewa ‘’shirme’’ ne.

Firmainistar kasar Giorgia Meloni wadda ta bayyana Italiya da ‘’mai arzikin abinci’’ ta samar da ma’aikatar abinci ta Italiya a lokacin da aka zabe ta, manufar hakan shi ne tsare abincin al’adun kasar.

‘’Abincin da aka samar da sinadarin kwari na ci gaba da bayyana a manyan kantunan sayar da kayayyaki a kasar’’, kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo.

Yayin da ake ci gaba da samun damuwa kan cewa ko kwari na cikin abincin kasar na al’ada, ministocin kasar uku sun bullo da wasu dokoki hudu na nufin soke wanna tunani.

‘’A bayyana take cewa wannan baya daga cikin abincinmu na al’ada.’’, in ji ministan noman kasar Francesco Lollobrigida.

Ba Italiya kadai ce ake samun rarrabuwar kawuna kan abincin da aka yi da sinadarin kwari ba.

A kasar Poland lamarin ya zama wani gagarumin batu da ya mamaye yakin neman zabe, gabanin babban zaben kasar da ke tafe cikin wannan shekara.

A watan Maris duk 'yan takarar manyan jam'iyyun kasar sun zargi juna da bullo da tsare-tsaren da za su tilasta wa 'yan kasar cin kwari.

Shugaban babbar jam'iyyar adawa Donald Tusk ya kira gwamnatin kasar da ''mai samar da miyar gwazarma''.

Haka kuma kasashen Austriya da Belgium da Netherland sun yi fice wajen cin abincin kwari, al'ummar Austriya na cin soyayyun kwari, ita kuma Belgium fitacciya ce wajen cin miyar gwazarma da sauransu.

A yayin da yawan al’umar duniya ya zarta biliyan takwas, akwai fargabar samun karancin abinci ga mutane masu yawa.

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole a kara zuba jari a harkokin noma da kashi 70 cikin 100.

Kuma dole a sauya akalar neman abinci mai gina jiki zuwa sauran abinci kamar nau'in kwari.

A baya damar samarwa ko sayar da abincin kwari a kayyade take.

To amma a yanzu da Tarayyar Turai ta amince da kwarin a matsayin abincin dan adam, ana tunanin cewa bangaren zai bunkasa, ta yadda farashin zai rika sauka sannu a hankali.

Source: BBC