A farkon makon nan ne, hotunan wata dattijuwar Baturiya rike da allon saukar karatun al-Kur'ani mai zayyana, cikin shigar hijabi, suka cika shafukan sada zumunta.
Mutane sun yi ta bayyana sakonnin taya murna da fatan alheri ga Malama Liliana Mohammed saboda wannan gagarumar bajinta da ta yi a rayuwa.
Ba a dai cika samun masu yawan shekaru da ke yin saukar Al-kur'ani ba.
To ko wace ce dattijuwa Liliana Mohammed?
Ga abu biyar game da rayuwarta:
Kuma dattijuwar ta haifi 'ya'ya biyu.
Liliana Mohammed ta yi bikin saukar Kur'ani ne tare da sauran daliban makarantar Islamiyya ta Mamba’irrahman a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba.
Ta ce yanayi a birnin Kano, na da karfafa gwiwar ayyukan ibada na addinin Musulunci, musamman idan ta kwatanta da kasar da ta fito.
"Ta fuskar lokaci. Lokutan sallah da na azumi sun dace matuka. Tsawon dare da na rana, kusan daya ne. Ba kamar wani sashen na duniya ba, inda ake da sa'a biyar kawai a lokacin dare."
Ta ce shi kansa yanayin muhalli a Kano yana da burgewa da karfafa gwiwa. A lokacin kiran sallah, duk inda mutum yake zai ji. Ta ce hakan yana da karfafa gwiwa, sannan ga mutane a ko'ina suna sallah a lokaci.
Ita ma 'yar autar dattijuwar, Hamida Ibrahim Sambo ta ce sun yi matukar farin ciki da wannan cikar burin rayuwa na mahaifiyarsu.
A cewarta shi ne muhimmin abin farin ciki da ya samu rayuwar danginsu.
"Hakikanin gaskiya ma shi ne abin da ya fi sanya su farin ciki a duniya. Haihuwa, aure duk ba su kawo wannan farin cikin ba, irin na Musuluncin da ta karba."
Hamida ta ce mahaifiyarta sun yi rayuwa da mahaifinsu wanda ya riga mu gidan gaskiya kimanin shekara 13 da ta wuce, ba tare da ta karbi Musulunci ba, sai da Allah ya yi masa rasuwa.
Ta yi ta maimaita kalmar godiya ga Allah. Tana cewa: "Alhamdulillahi! Ga shi yanzu tana iya daukan Kur'ani ta yi karatunta".
“Na fara karatu ne a gida, saboda yawan shekaruna. Mai koyar da ni Alkur'ani, Malama Hafsa, tana zuwa gida ne ta biya mini. Mun fara ne daga farko, inda take min rubutu da haruffan boko har zuwa lokacin da na fara gane haruffan Larabci.
“Ita ce ta ci gaba da koyar da ni karatun Kur'ani da haruffan Larabci har na zo na fara iya karantawa da kaina."
Liliana ta ce daga nan, sai suka ci gaba, ana biya mata karatu aya zuwa aya, sura bayan sura har zuwa ran da ta yi sauka.