Menu

Abu huɗu da Muhuyi zai binciki gwamnatin Ganduje a kai

Tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje (hagu) da Barista Muhuyi Magaji

Thu, 22 Jun 2023 Source: BBC

Shugaban hukumar sauraron ƙorafe-ƙorafen al'umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano watau PCACC, Barista Muhuyi Magaji ya ce zai gudanar da wasu jerin bincike a kan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da gwamnatinsa.

Daya daga cikin binciken da shugaban na yaki da rashawa a Kano yace zai mayar da hankali a kai shi ne binciken 'bidiyon dala'.

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi kan muƙaminsa nasa, bayan korarsa da tsohuwar gwamnatin jihar ta yi bisa dalilin cewa akwai shakku kan yanayin tafiyar da ayyukansa.

Sai dai kwana ɗaya bayan mayar da shi kan muƙamin, shugaban na PCACC ya shaida wa BBC cewar akwai wasu jerin zarge-zarge a kan gwamnatin Ganduje, waɗanda yake shirin buɗe bincike a kansu.

Ya ce "Za mu ɗora daga inda muka tsaya, dama akwai wasu bincike-bincike da muke yi wadanda daga baya wasu suke ganin ba za su yadda a ci gaba da yi ba saboda ya shafe su."

Lamarin ya fara tayar da ƙura ne bayan da Barista Muhuyi ya furta cewa hukumar 'za ta yi abin da ya kamata' a kan batun bidiyon zargin karɓar maƙudan kuɗaɗen dalar Amurka da ake yi wa tsohon gwamnan na jihar Kano.

Tun a lokacin da bidiyon ya fito, Ganduje ya musanta karbar rashawa inda yace siyasa ce kawai.

Sai dai ya ce ba bidiyon dala ne kawai zarge-zargen da ke kan tsohon gwamnan ba.

Bidiyon dala

Muhuyi Magaji ya ce ɗaya daga cikin manyan abin da zai mayar da hankali bayan komawa kan muƙaminsa shi ne bincike kan wani bidiyo, wanda ake zargin cewa, a cikinsa, tsohon gwamnan jihar Kano ne Abdullahi Umar Ganduje yake karɓar kuɗaɗen ƙasashen waje daga wani mutum.

Bidiyon wanda aka fitar a shekara ta 2018 da ya janyo cece-ku-ce, ba ma a jihar Kano kawai ba, har ma da Najeriya baki ɗaya, abin da ya kai ga majalisar dokokin jihar kafa kwamiti domin binciken gaskiyar lamarin.

Sai dai tsohon gwamnan a wata tattaunawa da BBC ya bidiyon da aka fitar ba gaskiya ba ne.

Ya bayyana lamarin a matsayin wata maƙarƙashiya ta hana shi cin zaɓe.

A bayanin nasa, Muhuyi ya ce za a yi bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin da kuma kare kimar jihar Kano.

Kuɗin haraji

Barista Muhuyi ya ce ɗaya daga cikin manyan abubuwan da zai yi binciken a kan su akwai batun haraji, inda ya yi zargin cewa wasu na kwashe kuɗaɗen da ake tarawa na al'umma jihar.

Ya ce idan har aka gyara ɓangaren tattara haraji na jihar, to Kano za ta samu damar gudanar da ayyukan ci gaba ba tare da sai ta ciyo bashi ba.

Akwai wasu ƙorafe-ƙorafe kan yadda gwamnati ta bai wa wasu kamfanoni kwangilar karɓar haraji.

Inda ake zargin cewa akwai alamar tambaya kan yadda ake raba kuɗaɗen tsakanin kamfanonin da gwamnatin jihar.

Kwangiloli

Shugaban na hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Kano ya ce akwai wasu kwangiloli da aka bayar a jihar wadanda aka yi ba bisa ƙa'ida ba.

Ya ce an rinƙa bayar da kwangilolin ne 'domin biya wa kai buƙata."

Wasu dai na zargin cewa ana yin ƙarya a farashin kwangiloli wanda ke ƙara karfafa ayyukan rashawa.

Zargin zuƙaƙa kuɗi a wajen bayar da kwangila lamari ne da ya yawaita a Najeriyar, inda ake zargin masu mulki da amfani da irin wannan dama wajen halastawa kansu kudin haram.

Kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Shugaban na hukumar PCACC ya ce akwai wani bincike da ya fara a baya kan batun kuɗaɗen ƙananan hukumo.

A cewarsa "Ana saka wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu na 'garant' a banki, daga nan sai su kuma su ɗauko kuɗin su kawo su cash (tsaba), ga wasu jami'an gwamnatin jihar."

A Najeriya dai, ana zargin gwamnatocin jihohi da yin sama-da-faɗi da kuɗaɗen da ake ware wa ƙananan hukumomi.

Lamarin da kai ga kiraye-kirayen bai wa ƙananan hukumomin ƴancin zaman kansu.

Sai dai duk da cewa shugaban ƙasa ya amince da ƴancin na ƙananan hukumomi, lamarin ya gaza samun goyon baya a matakin jihohi.

Tun bayan sanarwar dawo da Muhuyi Magaji kan muƙaminsa na shugaban hukumar sauraron ƙorafi da yaƙi da ayyukan rashawar ta Kano mutane ke bayyana ra'ayoyi da dama ganin cewar ba a yi rabuwar arziƙi ba tsakanin tsohon gwamna Ganduje da kuma shugaban na hukumar PCACC.

Haka nan kayen da ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC ya sha a hannun Abba Kabir na NNPP lamari ne da bai yi wa tsohon gwamnan daɗi ba.

Tuni dai gwamnati mai ci ta fara warware wasu daga cikin abubuwan da tsohuwar gwamnatin ta ƙulla, kamar rushe gine-gine da take iƙirarin an yi su ba bisa ƙa'ida ba.

Source: BBC