Watan Ramadan, lokaci ne da al'ummar musulmai ke rige-rigen aikata ayyukan alheri domin neman kusanci ga Allah SWT.
To sai dai bayan wucewar watan azumin, wasu mutane kan tsayar da ayyukan alkairin da suka faro cikin Ramadan, wanda kuma ba haka aka so ba.
Malamai suna cewa an fi so mutum ya ci gaba da ayyukan alherin da ya faro cikin Ramadan ɗin, domin kuwa a cewar malaman yin hakan alama ce da ke nuna azumin mutum ya karɓu.
Sheikh Sulaiman Datti babban limamin masallacin sunnah na Birnin Kudu a jihar Jigawa ya ce ya kamata mutum ya siffantu da ɗabi'u kyawawa waɗanda ya koya a cikin watan azumin har bayan azumin.
Malamin ya ce magabata kan shafe wata shida suna addu'a Allah ya kai su Ramadan, domin dacewa da alkairan da ke cikin watan.
A wannan maƙalar mun kawo muku abubuwa guda shida da za su taimaka muku wajen dorewa da ayyukan alherin da kuka faro a cikin watan.
Yawaita azumin nafila
Sheikh Sulaiman Datti ya ce abu na farko da zai sa bawa ya ɗore da ayyukan alkairin da ya faro a cikin watan azumin shi ne ɗorewa da azumin nafila.
Wanda hakan ne zai sa ya ji kamar har yanzu a cikin Ramadan yake, abin da kuma zai sa ya ci gaba da aikata sauran kyawawan ɗabi'u ko ayyukan da ya faro a lokacin azumin.
''Abin da zai nuna haka shi ne mutum ya dage da azumin nafila kamar na Sitta Shawwal, da azumin Litinin da Alhamis, da azumin Tasu'a da Ashura da azumin ranar Arfa, da azumin kwana uku a kowanne wata'', in ji Sheikh Sulaiman Datti.
'Ka ɗauka duka rayuwarka Ramadan ne'
Abu na gaba da mutum zai yi don ɗorewar ayyukan alheri shi ne mutum ya ɗauka a ransa cewa duka rayuwarsa gaba-ɗayanta Ramadan ne, in ji Sheikh Sulaiman Datti.
Malamin ya ce yin hakan zai sa mutum ya guje wa aikata miyagun laifuka bayan watan.
''Idan mutum ya ɗauka a ransa cewa koyaushe ma Ramadan ne, to hakan zai taimake shi wajen ci gaba da aikata ayyuka na alkairi''. in ji babban limamin na masallacin sunnah da ke Birnin Kudu.
'Kada ka bari Ramadan ya tafi da ayyukanka na alheri'
Sheikh Sulaiman Datti ya ce kada mutum ya yadda ya koma mai saɓon Allah bayan wucewar watan Ramadan.
''Wani daga cikin magabata yana cewa rashin rabo ya tabbata ga dukkanin mutumin da bai bari Ramadana ya tafi da sallarsa da azuminsa da kiyamul-lailinsa da sauran ayyukan da yake aikatawa na alkairi'', in ji malamin.
Gujewa aikata saɓo
Wani abu kuma da mutum zai yi don ci gaba da gudanar da ayyukan alkairi shi ne gujewa saɓo kowanne iri.
Sheikh Sulaiman Datti ya ce ya kamata kowanne musulmi da ya jingine aikata laifuka ko saɓo sakamakon zuwan watan Ramadan, to ya tabbatar ya ɗore da gujewa saɓon.
Malamin ya ce hakan ne kawai zai taimaka wa mutum wajen rabuwa da munanan halaye ko ɗabi'u a rayuwarsa.
''Mutum ya tabbatar da guje wa aikata saɓo komi ƙanƙantarsa, domin kuwa saɓo na hana aikata kyawawan ayyuka'', in ji malamin.
'Ka ɗauki ibadar da za ka iya dawwama a kanta'
Kasancewar watan azumi lokaci ne da musulmai kan jajirce wajen yawaita aikata ayyukan alkairi da za su kusanta shi da Ubangiji maɗaukakin sarki, kamar yawaita sallolin nafila da karatun al'qur'ani da ciyarwa da sauran ayyukan alheri.
A nan Sheikh Sulaiman Datti ya ce akwai hadisin da Manzon Allah SWT ke cewa ''idan za ku yi ibada to ku ɗauki wadda za ku iya yi''.
''Don haka idan ka san za ka iya yin nafila raka'a biyu-biyu a kowanne dare, to ka riƙi yin hakan, kar ka yadda ka ɗauki fiye da haka, dan kar ka je ka gajiya'', in ji malamin.
Malamin ya ce akwai hadisin da Manzon Allah ke cewa ''Aikin da Allah ya fi so na ibada daga wajen mutane, shi ne aikin da mutum ya dawwama yana aikatawa ko da kuwa ɗan kaɗan ne''.
Sheikh Sulaiman Datti ya ce alal misali idan mutum na saukar Qur'ani a sati cikin azumi, to a wajen azumi ya mayar da shi zuwa sati uku ko huɗu.
''Haka nan idan mutum a cikin azumi yana nafila raka'a 20 fiye to ya dage ko da raka'a biyu a kowanne dare ya riƙa yi'', in ji babban limamin.
Dagewa da tuba
Sannan kuma hanya ta shida da malamin ya bayyana ita ce yawaita tuba da istigifari.
''Yawaita tuba da istigifari hanya ce da take kusanta bawa da Ubangijinsa'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa ''Dole ne mutum ya dage da tuba da istigifari daga laifukan da yake aikatawa, domin kuwa zunubi na hana mutum ci gaba da aikata ayyuka na alkairi''.