Menu

Abubuwan ci gaba da Majalisar Dokokin Najeriya ta tara ta samar

Femi Gbajabiamila . Femi Gbajabiamila, Shugaban Majalisar Dokokin Najeriya

Fri, 9 Jun 2023 Source: BBC

Yayin da Majalisar Wakilan Najeriya ta tara zata yi zamanta na karshe bayan kama aiki a ranar 11 ga watan Yunin 2019, wasu ‘yan majalisar sun ce ta taka rawa sosai wajen bayar da shawarwarin da suka haifar da ci gaba a Najeriya.

Hon. Kabiru Alasan Rurum, daya ne daga cikin ‘yan majalisar da ya shaida wa BBC cewa, majalisar tasu ta tara karkashin jagoranci Femi Gbajabiamila, ta taka rawa daidai gwargwado musamman wajen tabbatar da an yi abubuwan raya kasa.

Ya ce, "Majalisarmu ta yi kokari wajen tabbatar da ganin an aiwatar da ayyukan raya kasa musamman na tsohuwar gwamnatin da ta shude da kuma tabbatar da an yi abubuwan da suka dace a bangarori da dama ciki har da bangaren tsaro."

Dan majalisar ya ce, "Kusan kowane bangare idan aka duba majalisarmu ta taka rawar gani, misali, a lokacin da matsalolin tsaro suka ta’azzara, majalisarmu ta yi kokari wajen matsawa a sauya shugabannin tsaro, sai da aka kai ruwa rana sannan daga karshe aka yi abin da muka bukata.”

Hon. Kabiru Alasan Rurum, ya ce bayan wannan, ko a lokacin da aka samu bullar annobar korona, majalisar ta tara ta bayar da shawarwari, sannan ta amince da kasafin kudi na musamman wajen tabbatar da cewa an tallafawa ‘yan kasa da kuma samar da kayan kula da marasa lafiya sosai.

"A bangaren noma ma, majalisarmu ta inganta harkar, musamman samar da a dokoki da suka baiwa shugaban kasa dama wajen cimma muradansa da suka hada da bunkasa noman shinkafa da aka yi a Najeriya" in ji Rurum.

Dan majalisar ya ce a kowane lokaci idan matsaloli suka taso musamman na yajin aiki a bangaren ‘yan kwadago ko ma’aikatan lafiya ko ma malaman jami’oi, shugabancin majalisa su kan zauna su shiga tsakani don a samu fahimtar juna.

Rurum ya kara da cewa "daga cikin irin nasarorin da majalisarmu ta samu akwai batun dokokin zabe da aka ingantasu sannan ga dokokin da muka yi a kan inganta harkokin man fetur na kasa da dai makamantansu".

Har'ilayau, ya ce, ‘"daga bangaren kalubale kuwa, akwai rashin wadatattun kudin da ‘yan majalisar zasu rika amfani da su wajen bibiyar ayyukan da bangaren zartarwa ke yi; Sannan kuma akwai wasu wurare da ya kamata a ce majalisa tana da karfin fada a ji amma ba ta samu wannan damar ba".

A ranar Laraba, 7 ga watan Yunin 2023 ne majalisar wakilan Najeriyar za ta yi zaman ta na karshe, yayin da ita kuwa takwararta ta dattawa za ta yi zaman karshe a ranar 8 ga watan Yunin 2023.

Source: BBC