Menu

Abubuwan da suka faru a Premier League a karshen mako

21490791 Premier League trophy

Mon, 24 Oct 2022 Source: BBC

A karshen mako aka yi wasannin sati na 13 a gasar Premier League, inda za a karkare da karawa tsakanin West Ham da Bournemouth ranar Litinin. West Ham tana ta 17 da maki 11, bayan buga karawa 11, ita kuwa Bournemouth mai maki 13 tana mataki na 13, bayan wasa 11 da ta buga a Premier. Ga jerin wadansu abubuwan da suka faru a karshen makon DE BRUYNE YA KOMA CIKIN MASU CIN KWALLO Kevin De Bruyne ya taka rawar gani a wasan da Manchester City ta doke Brighton 3-1, inda ya ci na uku daga ciki. Kwallo na biyu kenan da dan wasan ya zura a raga tun ranar 13 ga watan Agusta da ya zura daya a fafatawar da City ta sharara kwallo 4-0 a ragar Bournemouth. De Bruyne shi ne kan gaba a yawan bayar da kwallaye a zura a raga a Premier mai tara mai 11 jumulla a dukkan fafatawa. TOTTENHAM NA BUKATAR KULUSEVSKI YA KOMA BUGA MATA WASANNI Bayan da Tottenham ta fara kaka mai kayatarwa bayan wasa 10 a Premier a bana a karon farko tun 1963, kungiyar ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere a yanzu haka. Kungiyar ta yi rashin nasara a Manchester United, sannan ranar Lahadi Newcastle ta je har gidan Tottenham ta doke ta da ci 2-1. Kungiyar da Antonio Conte ke jan ragama ba ta buga wasa mai armashi, wasu na ganin rashin Dejan Kulusevski ne wanda ke jinya. Dan kwallon ya buga rabin wasan da Tottenham ta yi daga 12 a Premier League, inda ba a ci kungiyar ba a karawar da ya yi mata. Tun bayan da ya ji rauni Tottenham ta buga wasa shida ta yi nasara a uku da shan kashi a karawa uku. Rashin dan wasan ne ya shafi kwazon Tottenham, wadda ke bukatar Kulusevski ya murmure ya koma taka mata leda, domin ta ci gaba da zama a kan ganiya. VILLA TA FARA DA KAFAR DAMA BAYAN KORAR GERRARD Aston Villa ta koma cin wasa a Premier League, bayan da ta kori Steven Gerrard. Aston Villa karkashin kociyan rikon kwarya, Aaron Danks ta sharara kwallo 4-0 a ragar Brentford, inda tun a minti na 14 ta zura uku a raga a Villa Park. Danks ya zama kociyan Aston Villa na farko da ya ci wasan farko da kwallaye 4-0. Villa ta sallami Gerrard ranal Alhamis, bayan da Fulham ta yi nasara da ci 3-0 a gasar Premier, kocin da ya ci wasa 13 aka doke shi 19 a karawa 40 da ya ja ragama tun daga 11 ga watan Disambar 2021. KWAZON ARSENAL YA YI KASA A SOUTHAMPTON Kociyan Arsenal, Mikel Arteta bai ji dadin rashin kwazo da 'yan wasansa suka sa a karawa da suka tashi 1-1 da Southampton a St Mary ranar Lahadi. Arsenal ce ta fara cin kwallo da fara wasa, daga baya Southampton ta farke bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu. Arsenal wadda ta fara kakar bana da bajinta, wadda ta fara cin kwallo ta kasa taka rawar da ya kamata a matakin mai shirin lashe kofin Premier na bana. Wasu na cewar 'yan wasan Arsenal sun gaji ba su samu hutun da suke bukata ba, bayan doke PSV Eindhoven a gasar Europa League. Hakan ya sa Southampton daga baya ta dunga murza leda son ranta, sai dai hakan gargadi ne ga Arteta cewar sai ya kara sa kwazo, idan ba haka ba Manchester City ta karbe gurbin matakin farko, kuma sauke ta sai an yi da gaske. KUNGIYAR WOLVES NA KARA FUSKANTAR KALUBALE Wolverhampton Wanderers ta koma ta 19 a kasan teburi, bayan wasa 12 da maki tara a gasar Premier ta bana. Watakila kungiyar ta yi kuskure da ta ce za ta bar Steve Davis aikin kociyan rikon kwarya har lokacin da za a fara gasar kofin duniya. Ranar Lahadi Leicester City ta doke Wolverhampton 4-0 a Molineux, kenan kungiyar ta sha kashi a wasa biyar daga shida da ta yi bayan nan. Bayan da Wolves ta yi nasara a kan Nottingham Forest, Leicester wadda take ta karshen teburi ta dura mata kwallaye a ranar Lahadi. Kwallo biyar kacal ta zura a raga a bana, ita ce mai karancin kwallaye da babu mamaki da kungiyar ke cikin 'yan ukun karshe a kakar nan.

Source: BBC