Hukumar alhazai ta Najeriya fito da tsarin adashin gata, da zai bai wa maniyyata aikin Hajji, masu karfi da marasa karfi damar tara kudin zuwa kasa mai tsarki.
Manufar wannan tsari shi ne saukakawa maniyyata wajen tara kudin gwargwadon halin da mutum yake da shi.
Hukumar alhazai ta dauko wannan tsari na adashin gata daga kasashe kamar Malaysia da Indonesia, inda 'yan kasar ke irin wannan tarin kudi don sauke faralli.
Shugaban sashen adashin gata na hukumar Alhazan Najeriyar Aliyu Tanko ya shaida wa BBC cewa akwai hanyoyi guda uku da wadanda ke son shiga tsarin adashin gata za su bi, domin cin gajiyar shi.
Kuma fatanmu shi ne idan kudin mutum sun rage, za mu ba shi idan ya dawo daga aikin Hajji domin ya juya su ta hanyar yin wani kasuwanci, idan kuma yana so zai iya ci gaba da adashin gata na komawa aikin hajji ko biya wa wani dan uwansa,'' in ji Aliyu Tanko.
Shin ko adashin gata ya shafi mazauna karkaka?
Shugaban sashen adashin gatar ya ce: ''Kawo yanzu ba a shigar da tsarin ma'aikatan hukumar alhazai ko na bankin Ja'iz su shiga kauyuka don karbar kudin shiga adashin gata ba.
"Amma suna da damar shigo birni don zuwa banki ko hukumar alhazai da kansu don shiga tsarin.''
Mece ce makomar wanda ya rasu ya na tsarin adashin gata?
'Dr Tanko ya ce: 'Idan mutum yana cikin tara kudin Allah ya yi masa rasuwa, magada na da damar zuwa kotu su bukaci yadda suke son kudin ya kasance, ko dai a ba su kudin su raba shi a matsayin gado ko su wakilta mutum guda da zai maye gurbin mahaifinsu sai mu sauya suna.
Sannan ba wai wanda ya rasu kadai ba, mutum yana da damar dawowa hukumarmu don sauya sunan wanda yake son ya ci gajiyar adashin. Ko dai dansa ko mata ko ma duk wanda yake son maye gurbinsa.
Ya ce fatansu shi ne tsarin ya kawo sauyi ta fannin sauko da farashin kudin aikin Hajji, da sauya wa mahajjata masauki su kusanci da Masallatan Harami na Makka da Madina.
Dr Tanko ya kara da cewa suna kuma fatan kawo damar samun saukin farashin kudin jirgi, "tsari ne da muke fatan ya kawo sauyin da zai saukaka wa 'yan Najeriya a lokacin aikin hajji."