Benfica ta je Inter Milan buga wasa na biyu a quarter finals a Champions League, bayan da aka doke ta 2-0 a makon jita.
Ranar 11 ga watan Afirilu, Inter ta doke Benfica 2-0 a wasan farko a Portugal, Nicolo Barella ya fara cin kwallo, sannan Romelu Lukaku ya ci na biyu a fenariti.
Daga wasa tara da aka ci Benfica kwallo biyu ko fiye da hakan a wasan farko sau daya ne kungiyar Portugal ta kai zagayen gaba.
Shine wanda Nurnberg tta ci 3-1 a wasan farko, Benfica ta sharara 6-0 a fafatawa ta biyu a kakar 1961-62.
To sai dai ba a doke Benfica a wasa bakwai baya ba da ta buga a waje, idan ka cire wanda ta yi a cikin rukuni a bana a Champions League.
A karawa hudu da suka yi a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, Inter ta yi nasara a wasa uku da canjaras daya - kenan akwai jan aiki a gaban Benfica kenan.
Wadanda za su iya buga wasan:
Inter: Onana; Darmian, Acerbi, Bastoni; Dumfries, Barella, Hakan Çalhanoğlu, Mkhitaryan, Dimarco; Džeko, Martínez
Wadanda ba za su buga wasan gaba idan aka yi musu katin gargadi: Bastoni, Dimarco, Džeko, Martínez
Benfica: Vlachodimos; Gilberto, António Silva, Otamendi, Grimaldo; Florentino, Chiquinho; Aursnes, Rafa Silva, João Mário; Gonçalo Ramos
Wadanda ba za su buga wasan gaba idan aka yi musu katin gargadi: Gonçalo Ramos, Florentino, João Mário
Wasa tsakanin Benfica da Inter Milan:
Champions League Talata 11 ga watan Afirilu
UEFA Cup Alhamis 11 ga watan Maris 2004
Wannan shine wasan farko da Inter ta kai quarter finals tun bayan shekara 12, tun daga nan ba ta kara abin kirki ba, bayan lashe kofin a 2010.