BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Akwai jan aiki a gaban sabuwar gwamnatin da za a rantsar a Najeriya - Bafarawa

Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Sun, 21 May 2023 Source: BBC

Yayin da ya rage saura 'yan kwanaki kadan a rantsar da zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, wasu kusoshin babbar jam'iyyar hamayya ta kasar, wato PDP, na ganin akwai jan aiki a gaban sabuwar gwamnatin da ke tafe.

Cikin wata hira da BBC, Dakta Attahiru Dalhatu Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma jigo a jam'iyyar ta PDP, ya ce bai ga wani abin murna a kan batun rantsar da sabon shugaban kasa ba.

Ya ce, “ Bisa la’akari da yadda matsalar tsaro take addabar garuruwa da dama a yankin arewacin Najeriyar, da yadda matsalar ta gurgunta harkar noma, da kuma yadda hakan ke kara haddasa yunwa a tsakanin jama'ar yankin, banga abin murna don za a rantsar da sabon shugaban kas aba saboda jan aikin da ke gabansa.”

Bafarawa, ya ce yamakata gwamnati mai tafiya da wadda zata kama aiki, su yi maza su dauki matakin ganin hanyar da za abi talaka ya yi noma.

Tsohon gwamnan na Sokoto ya ce, ‘’ Matsawar ba ayi nom aba, to mulkin ma zai yi wuya ga duk wanda ya karbe shi, don sai da kwanciyar hankali mulkin ma ake iya yinsa.”

"Idan har aka bawa al’ummar arewa dama suka yi noma, to Allah zai taimakesu su tsaya da kafafunsu."

Amma duk wanda zai zo ya ce zai yi mulkin Najeriya ya bar talakawa cikin halin da suke ciki, to gaskiya akwai matsala, inji shi.

Dakta Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce wajibi ne sabuwar gwamnatin da za a rantsar ta duba wadannan matsaloli, kuma ta tanadi kwararan hanyoyin magance su, don talaka ya sami kyakkyawan sauyi a yanayin rayuwarsa.

Source: BBC